Mun yi imani da
cewa Allah zai tayar da mutane bayan mutuwarsu a wata sabuwar halitta a ranar
da aka yi wa bayi alkawari game da shi. Kuma zai saka wa masu biyayya ya
azabtar da masu sabo.
Wannan al'amari ne
da baki dayansa da abinda ya tattara akai dangane da abinda wanda saukakkun
shari'o'i da masana Falsafa suka yi ittifaki a kai. Babu wata gujewa ga musulmi
ya yi ikrari da akidar Alkur'ani wadda Annabinmu mai girma ya zo da ita
(S.A.W.A), domin wanda ya yi imani da Allah, imani tabbatacce to kuwa ya yi
imani da Muhammadu (S.A.W.A) a matsayin manzo daga gare shi wanda ya aiko shi
da shiriya da addini na gaskiya haka kuma babu makawa ya yi imani da abinda
Alkur'ani ya ba da labarinsa game da tashin kiyama, da sakamako da azaba, da
aljanna da ni'ima, da wuta da kuma Alkur'ani ya bayyana haka a sarari kuma yayi
ishara da shi a cikin abinda ya kai kimanin aya dubu.
Idan har shakku ya shigi wani game da haka babu
wani abu sai dai saboda shakkun da yake da shi game da ma'abucin sakon, ko kuma
ma game da samuwar Mahaliccin halittu da kudurarSa, bil hasali ma sai dai da
shakkun da yake bullo masa game da asalin addinai baki dayansu, da kuma
ingancin shari'o'i dungurungum.
Tayar da jikunna
Bayan wannan, tayar da jikkuna a kebe wani
al'amari ne da yake babu makawa daga cikin al'amuran addinin musulunci,
Alkur'ani mai girma ya yi ishara gare ta:
"Shin
mutum yana tsammanin ba za mu tattara kasusuwansa ba ne. E Lalle mu masu
kudurar madaidaita yatsunsa ne.[1]
"Idan
kayi al'ajabi to abin al'ajabi ce maganarsu eewa ashe idan muka zama turbaya za
a dawo da mu halitta sabuwa."[2]
"Shin
mun gajiya ne da halitta na farko a'a su dai suna cikin rudewa ne game da
sabuwar halitta."[3]
Tayar da jikkuna da ba wani abu ba ne illa sake
dawo da mutum ranar tashin kiyama, ranar fitowar shi da jikinsa bayan
rididdigewa da sake komar da shi zuwa ga kamarsa ta farko bayan ya zama
rididdigagge.
Ba wajibi ba ne a yi imani da filla-fillan
tayar da jikkuna fiye da wannan abinda a kan saukinta da Alkur'ani ya yi kira
game da ita a Alkur'ani, kuma mafi yawan abinda yake biye da ita na hisabi da
siradi, da auna aiki da Aljana da wuta, da sakamako da azaba duk gwargwadaon
abinda bayaninsa ya zo a Alkur'ani ne:
Bai wajaba ba sanin hakikancewar da babu mai kaiwa
gare ta sai ma'abucin zurfin nazari mai kaifi, kamar ilimin cewa shin jikkuna
zasu dawo ne da kan kansu ko kuma wasu makamantansu ne a sura? Kuma rayuka shin
za su gushe ne kamar jikkuna ne ko kuwa za su ci gaba da kasancewa har sai sun
sadu da jikkuna yayin tashin kiyama? Kuma cewa shin Tashin kiyama ya kebanta ga
mutum ne ko kuwa za a hada har da dukkan dabbobi ne? kuma shin komawa da su da
hukuncin Allah tashi daya ne ko kuma sannu sannu ne?
Kuma idan yin imani da Aljanna da wuta wajibi
ne to ba ya zama lalle a san da samuwarsu a halin yanzu da kuma sanin cewa suna
sama ne ko suna kasa ko kuma sun saba.[4]
Kazalika idan sanin ma'auni ya zama wajibi to
ba wajibi ba ne a san cewa ma'aunin na a surance ne ko kuwa yana gurin gwada
nauyi ne biyu.
Kuma ba lazimi ba
ne a san cewa siradi jiki ne siriri ko kuwa tsayuwar daka ce surantawa. Kuma
manufar dai ita ce cewa ba sharadi ba ne a yi binciken hakikancewa don sanin
cewa da jikkuna ne ko a'a..."
Na'am wannan akidar tashin kiyamar da saukin da
take tare da shi ita ce wadda musulunci ya zo da ita, idan mutum ya so ya
ketere shi zuwa filla-filla sosai fiye da yadda ya zo a Alkur'ani domin ya
gamsar da kansa don kore shakkun da masu bincike ke tayarwa ta hanyar dalilan
hankali ko kuma gwajin bincike- to lalle yana wahalar da kansa ne kawai, kuma
zai fada a cikin mushkiloli da rikice-rikice da jayayya marar iyaka.
A addini babu adinda ke kira zuwa ga wannan
zurfin binciken da littafan masu bincike game da Akida da malaman falsafa, kuma
babu wata larurar addini ko ta zamantakewa ko siyasa da ke kira zuwa ga irin
wadannan rubuce-rubuce da makalolin da ke cike da littafan haka nan a wasa, da
kuma wadanda suka kare karfin da kokarin masu jayayya da karfinsu da lokutansu
da tunaninsu ba tare da fa'ida ba.
Mushkiloli da shakkun da ake tasowa da su game
da filla-fillansu ya wadatar wajen raddinta mu yi imani da gazawar mutum game
da fahintar wadannan al'amura boyayyu daga gare mu, da kuma wadanda suke sama
da fahintarmu da samuwarmu, wadanda suka dara matsayinmu na kasa, tare da sanin
cewa Allah Ta'ala Mai iko ne a kan Ya ba mu labarin hakikanin aukuwar tashin
kiyama da tashin kabari.
Sanin dan'Adam da gwaje-gwajensa da
bincike-bincikensa ba zai yiwu su tabo wani abu da ba'a san shi ba su sanya shi
a karkashin gwajinsu da kwarewarsu ba sai dai bayan mutuwarsa da ficewarsa daga
wannan duniya ta majiyan jiki da gwaje-gwaje da bincike, to yaya za'a sa rai ya
yi hukunci da 'yancin tunaninsa, da kwarewarsa wajen kore wannan abu ko
tabbatar da shi? Ballantana ma game da filla-fillansa da kebantattun
al'amuransa sai dai idan ya dogara a kan bokanci da dikake da al'ajabi da ban
mamaki kawai kamar yadda yake a dabi'ar sake-saken zuciyar mutum ya yi mamakin
duk abinda bai saba da shi ba bai sami iliminsa da fahintarsa, kamar wanda ya
kore yiwuwar tashin Alkiyama da jahilcinsa yana mamaki da al'ajabin tashin
kiyama da fitowa daga kabari yana cewa: "Wane ne zai tayar da kasusuwa
alhali suna rididdigaggu."
Babu wata madogara
ga wannan mamaki sai dai kawai shi bai ganin matacce rididdigagge ba wanda aka
koma da shi rayuwa sabuwa. Sai dai kuma ya manta yadda aka halitta shi a karo
na farko ne, da ya kasance babu shi, gabobinsa da yankunan jikinsa riddidigaggu
daga yankunan kasa da abubuwan da ta kunsa, da kuma a cikin iska a warwatse nan
da can aka harhado shi har ya zama mutum daidai mai hankali; "Shin shi
mutum ba ya gani ne Mu Mun halitta shi daga digon maniyi sai ga shi yana mai
husuma bayyananne. Kuma ya ba Mu misali ya mance halittarsa."
Mai irin wannan
maganar sai a ce masa: "Zai raya shi, wannan da Ya fare shi a karo na
farko kuma shi masani ne game da dukkan halitta." [5]
Kuma a ce masu:
Kai lalle bayan ka san mahaliccin halittu da kudurarsa kuma ka san Manzo da
abinda ya ba da labari game da shi,tare da karancin saninka hatta ma fahimtar
sirrin halittarka da sirrin samar da kai, da kuma yadda ka girma da kuma yadda
ka fita daga marhalar digon maniyi da ba ya jin kome ba ya da hankali zuwa
marhalolin da ke biye da ake tattaro daga kwayoyi manesanta, domin ka zamanto
mutum daidaitacce mai hankali mai tuntuni mai ji na jiki da maganai.[6]
Bayan wannan kuma
sai a ce masa ta yaya kake mamakin komo da rayuwa sabuwa bayan zamantowa
rididdigagge, kana kokari da haka ka kai ga abinda kwarewar ka da iliminka suka
yi kadan wajen gano shi?
Sa'an nan a ce masa ba ka da wata mafita illa
ka mika wuya kana mai ikrari game da wannan hakika wadda Mai tafi da halittu
Masani Mai kudura game da ita, kuma Mahaliccinka daga babu kome da kuma abubuwa
rididdigaggu Ya bada labari kan aukuwarsa.
Duk wani kokari na binciko abinda ba za ka iya
gano shi ba, kuma iliminka ba zai kai gare shi ba, to kokari ne kawai na banza
da buga-buga a cikin rudu, da bude ido a cikin duhu mai halakarwa kawai.
Shi mutum duk da irin abinda ya kai gare shi na
ilimi da shekarun nan na karshe, Ya kago lantarki, da "rada", wato
na'urar hangen nesa, da masaniyar amfani da makamin kare dangi da dai sauran
irin wadannan kage-kagen da suka auku a shekarun baya-bayan nan wadanda idan da
an ba da labarinsu a da can to da an kidaya su a cikin abubuwan da ba za su
yiwu ba ya yi watsi da su ya wawaitar da su to har yanzu mutum bai san
hakikanin wutar lantarki ba da sirrin kwayar zarra, kai hatta ma hakikanin daya
daga cikin abubuwan da suka kebanta da su da siffofinsu, to yaya zai ji
tabbacin gano sirrin halitta da samuwa, sa'annan ya kara gaba yana so ya san
sirrin tashin kiyama da tashi daga kabari.
E, haka ne, ya kamata ga musulmi bayan ya yi
imani da Musulunci ya nesanci bin son zuciya kuma ya shagaltu a kan abinda zai
gyara al'amarinsa na duniya da lahira da kuma abinda zai daukaka masa
matsayinsa a gurin Allah, kuma ya yi tunani a kan abinda zai taimake shi a kan
son ransa da kuma abinda zai fuskanta bayan mutuwa na daga tsananin kabari da
hisabi bayan hallara a gaban mai Mulki Masani, kuma yaji tsoron "wata rana
da wani rai ba ya wadatarwa wani rai kome kuma ba a yarda da ceto gare shi,
kuma ba a karbar fansa gare shi kuma ba a taimakon su."[7]