Kira Zuwa Ga Hadin  kan musulmi

An san Ahlul Bait (A.S.) da kwadayinsu a kan wanzuwa da dorewar zahirin addinin Musulunci, da kira zuwa ga daukakarsa da hade kalmar mabiyansa, da kiyaye 'Yan'uwantaka a tsakaninsu da cire kufe daga zukata da kullaci daga rayuka.
Ba za a mance da matsayin Amirul Muminin Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) dangane da halifofin da suka gabace shi ba, duk da hujjar da yake da ita a kansu, da imaninsa cewa sun yi kwacen hakkinsa daga gare shi, amma ya zama tare da su ya zauna lafiya da su, kai hatta ma danne ra'ayinsa ya yi na kan cewa shi ne wanda aka nada da nassi a kan halifanci, har ma shi bai bayyana wani nassi ba a bainar jama'a ba har sai da al'amarin ya shigo hannunsa sa'an nan ya kafa hujja da sauran wadanda suka rage daga cikin Sahabbai game da al'amarin nassin Al-Ghadir sananniyar ranar nan ta Rahba.[1]
Ya kasance ba ya jinkirin yin ishara gare su game da abinda ya shafi musulmi da Musulunci wajen amfani da kuma fa'ida, kuma sauda yawa yana magana game da wannan alkawari: "Sai naji tsoron idan ban taimaki musulunci ba da ma'abutansa zan ga gibi a cikinsa ko rushewa."[2]
Kamar yadda babu wani abu da ya taba bullowa daga gare shi wanda zai yi tasiri a kan karfin mulkinsu, ko kuma ya raunana shugabancinsu ko kuma ya rage kwarjininsu sai ya kuntatawa kansa ya zauna a gida duk da abinda yake gani daga gare su.
Duk wannan saboda kiyaye maslahar addinin musulunci baki daya, da kariya kada a ga wani gibi a musulunci ko rusawa, har sai da aka san haka daga gare shi, kuma halifa Umar Bin Khattab ya kasance yana cewa:
"Kada na kasance gurin zaman da babu Baban Hasan a cikinsa Ko kuma, "Idan da ba don Ali ba to lalle da Umar ya halaka."[3]
Ba za a mance matsayin Imam Hasan bin Ali (A.S.) ba dangane da yin Sulhu da Mu'awiya ba,169 bayan ya ga cewa yaki zai cutar da nauyi mafi girma da kuma hukumar adalci kai hatta sunan Musulunci har zuwa karshen zamani a shafe shari'ar Ubangiji a kuma gama da wadanda suka saura da sauran zuriyar Manzo daga Ahlul Bait, sai ya fifita kiyaye zahirin Musulunci da kuma sunan addinin Musulunci inda ya yi sulhu da Mu'awiya babban makiyin addini da ma'abutansa, kuma abokin husumarsa, mai tsananin kiyayya gare shi da mabiyansa tare da abinda yake sa ran aukuwarsu na daga zalunci da wulakanci gare shi da mabiyansa. Sa'an nan kuma takubba Bani Hashim da takubban mabiyansu sun kasance a zazzare ba sa son komawa, ba tare da kwato hakkinsa da kariya tare da kuma maida martani ba, amma maslahar Musulunci madaukakiya ita ce ta fi kome daga cikin wadannan al'amuran a gurinsu.
Amma Husain Shahidi (A.S.) kuwa ya yunkura ne ba don kome ba sai don cewa idan aka ci gaba da halin da ake ciki ba a sha gabansu an sami wanda ya fallasa mummunar niyyarsu ba to da sannu za su shafe sunan musulunci, za su goge girmansa don haka ya so ya tabbatar wa tarihi ja'ircinsu da ketare iyakarsu, ya fallasa abinda suka kasance suna kukkula shi ga shari'ar Manzon Allah (S.A.W.A) abinda ya so kuma haka ya wakana. Idan da ba don Yunkurinsa ba to da musulunci ya zama sai sunansa a tarihi, a yi ta ambatonsa a tarihi tamkar wani addinin karya.
Kwadayin Shi'a a kan raya ambatonsa ta hanyoyi daban-daban kuwa saboda kammala Yunkurinsa ne na fafatawa da zalunci da jairci kuma domin raya al'amarinsa da al'amuran Imaman bayansa ne.
Kwadayin Ahlul Bati (A.S.) wajen ci gaba da daukakar addinin musulunci -koda kuwa masu shugabincin al'umma matsananta makiya ne gare su kuwa.
Matsayin Imam Zainul Abidin (A.S.) game da sarakunan Banu Umayya alhali yana cikin rashin kwanciyar hankali game da su, kuma a zamaninsu ne aka keta martabarsa da mutuncinsa, kuma da'iman yana cikin kunci da damuwar abinda suka yi wa mahaifinsa a abinda ya auku a Karbala, amma duk da haka Shi a koyaushe yana addu'a ga sojojin musulmi a asirce don su sami cin nasara; musulunci kuma ya daukaka, musulmi kuma su sami karfafa da aminci, ya riga ya gabata cewa makaminsa kawai wajen yada ilimi shi ne addu'a. Ya koya wa Shi'a yadda za su yi addu'a ga sojojin musulunci da musulmi wato kamar addu'arsa sananniya mai suna, "Addu'a ga ma'abuta dakon iyaka" wadda yake cewa:
"Ya Allah ka yi dadin tsira ga Muhammadau da zuriyar Muhammadu, kuma Ka yawaita adadinsu, Ka kaifafa makamansu, Ka kare martabarsu, Ka kange iyakarsu, Ka hado taronsu, Ka shirya al'amarinsu, Ka bibiyar da tsakanin abin masarfinsu, Ka kadaita da wadatar da bukatunsu, Ka karfafa su da cin nasara, Ka taimake su da hakuri, Ka tausasa musu wajen shiri,"
Har zuwa inda yake cewa: "Ya Allah Ka karfafa guraren musulunci da haka, Ka kiyaye gidajensu da shi, Ka yada dukiyarsu da shi, Ka raba su da yakayya su dukufa ga ibadarKa, da kuma hana ja da su har kadaita da kai, har ya zamanto ba a bauta wa kowa a doron kasa sai Kai, kuma babu wani mai gafarta wa wani daga cikinsu sai Kai."
Haka nan yake ci gaba da addu'arsa mai zurfi -kuma tana cikin addu'o'insa mafiya tsawo- wajen fuskantar da sojojin musulunci zuwa ga abinda ya kamace su na daga manyan kyawawan dabi'u da kuma shirya kansu a kan makiya, ta kunshi dukkan darussan yaki a jihadin musulunci da bayanin manufarsa da fa'idarsa kamar kuma yadda take fadakar da musulmi da irin shirin da ya kamata su zauna da shi dangane da makiyansu da ya wajaba su yi wajen mu'amala da fuskantarsu da kuma abinda ya wajaba a kansu game da yankewa daga kome da juyawa ga Allah baki daya da nesantar abubuwan da ya haramta da yin abu saboda Shi kawai.
Kamar kuma sauran Imaman (A.S.) game da matsayinsu dangane da sarakunan zamaninsu, duk kuwa da cewa sun fuskanci matsa lamba da azabtarwa mai tsanani daga gare su, saboda ya yin da suka san cewa hukumar adalci ba za ta dawo gare su ba sai suka dukufa da koya wa mutane al'amuran addinin suna faskantar da mabiyansu fuskantawa ta addini madaukaki.
Dukkan wani juyi da ya auku a zamaninsu daga bangaren Alawiyawa da wasunsu bai kasance da ishararsu da koyarwarsu ba bil hasali duk sabanin umarninsu ne a bayyane da tsanantawarsu, duk da cewa su sun kasance sun fi kowa kwadayin kafa hukuma hatta halifofin Bani Abbas.
Karanta wasiyyar Imam Musa Bin Ja'afar (A.S.) ga Shi'a mabiyansa: "Kada ku dukar da wuyanku da barin biyayyar shugabanku domin idan ya kasance mai adalci to ku roki Allah ci gabansa, idan kuwa ya kasance ja'iri to ku roki Allah gyaransa, domin gyaruwarku na cikin gyaruwar shugabanku, kuma lalle shugaba tamkar uba mai rahama yake, ku so masa abinda kuke so wa kanku kuma ku ki masa abinda kuke ki wa kanku."[4]
Wannan shi ne matukar abinda ake so na kiyayewar ababa kulawa da su, talakawa, game da lafiyar Shugaba wato su so masa abinda suke so wa kansu su ki masa abinda suke ki wa kansu.
Kuma bayan duk wannan laifin wasu marubutan wannan zamani ya girmama wadanda suke cewa wai Shi'a wata jam'iyyar Asiri ce mai tabargaza ko kuma wata kungiyar 'Yan juyin juya hali masu ramuwar gayya.
Gaskiya ne cewa dabi'ar musulmi mai bin kayarwar Ahlul Bait (A.S.) ita ce kiyayya da zalunci da azzalumai da kuma nesantar ma'abuta ja'irci da fasikanci tare da duban mataimakansu da mabiyansu da duban kyama da kiyayya da rashin yarda da wulakanci. Wannan hali bai gushe ba yana tare da su suna gadonsa zuriya bayan zuriya amma duk da haka ba dabi'arsu ba ne kisan gilla ko kisan yaudara ba, kuma ba ta hanyarsu juyin juya hali da yunkurawa a kan wata hukuma mai jagoranci da sunan addini, ba sa yi a asirce ba sa yi a bayyane, kuma ba sa halattawa kansu kisan gilla ko kwanton bauna ga musulmi koda wace irin mazhaba ko darika yake bi kuwa, suna masu riko da koyawar Imamansu (A.S.).
Bilhasali duk wani musulmi da ke shaidawa da kalmar Shahada biyu to dukiyarsa ta tsira jininsa ya kubuta kuma mutuncinsa katangagge ne. "Dukiyar mutum musulmi ba ta halatta sai dai da son ransa."[5]
Bil hasali ma musulmi dan'uwan musulmi ne kuma hakkokin 'Yan'uwantaka na kansa wadannan bayanin da ke biye zai fayyace su.


[1] Musnad Ahmad Juzu'i na 1: 83, Fadha'ilu Ahmad shafi na 77 hadisi na 115, Sunan Ibin Ali Asim: shafi na 593 hadisi na 1372 da 1373 da 1374, Mushkilul Asar Juzu'i na 2 shafi na 307, da Khasa'is Na Nisa'i shafi na 100 da 101 hadisi na 85-86 da Al- Mu'ujamus Sagir na Tabarani Juzu'i na 1 shafi na 65, da Al-Mu'ujamul Wasit Juzu'i na 2 shafi na 68 da Hulliyatul Awliya' Juzu'i na 5 shafi na 26, da Al-Manakib na Ibin Magazilli shafi na 20 hadisi na 28, Kanzul Ummal Juzu'i na 13 shafi na 157 hadisi na 36485, 36486, shafi na 170 hadisi na 36514, Usudul Gaba Juzu'i na 3/321, 4/28.
[2]Nahjul Balagah: al-Kitab 62 (min kitabin lahu alaihis salam ila Ahlul Basra).
[3]Tabakat na Ibin Sa'ad, Juzu'i na 2 shafi na 339 Fada'ilu Ahmad, shafi na 1 55 hadisi na 222, da Insabul Asharaf na Balaziri Juzu'i na 2 shafi na 99 hadisi na 29 Sharhin Nahjul Balagha Ibin Abil Hadid Juzu'i na 1 shafi na 18, Al- Manakib na Khawarzimi shafi na 96-97 karshen hadisi na 97 da 98, da Usudul Ghaba Juzu'i na 4 Shafi na 22, Kifatut Talib shafi na 217, Al- Isaba Juzu'i na 2 shafi na 509, Zakha'irul Akaba shafi na 82, Tahzibut Tahzib Juzu'i na 7 shafi na 296, Tazkiratul Khawas shafi na 134 da 137 da Riyadun Nadrah Juzu'i na 3 shafi na 161 da Fara'idus Samtin Juzu'i na 1 shafi na 344 hadisi na 267.
[4] Al- Manakib na Khawarzimi shafi na 80 hadisi na 65, Tazkiratul Khawas shafi na 137, Sharhin Nahjul Balagha Ibin Abil Hadid shafi na 18 da 141, da 12, 179, da 223 Kifayatut Talib 219 Zakai'rul Akaba shafi na 82, da Riyadun Nadrah Juzu'i na 3, shafi na 161.
[5] Za a iya duba sulhun da ya auku tsakanin Imam Hasan (A.S.) da Mu'awuya ta kusurwoyi daban-daban, daga ciki akwai:
Na farko: Karya shamakin ruhin da Mu'awuya ya yi kokarin ya nuna wa musulmi baki daya dangane da nacewasa a kan sulhu domin ya yaudari mutane, Imam Hasan (A.S.) Ya bayyana uzurinsa tun farko cewa Mu'awuya ba zai yi aiki da sharudansa ba kuma ba amintacce ba ne a kan addini da kuma al'umma.
Na Biyu: Idan da Imam Hasan (A.S.) Ya dage da ci gaba da yaki da Mu'awuya to da yakin ya kazanta kwarai kuma da ya kai ga halaka Imam din da dukkan Bani Hashim kuma da an cire shi da bangaren masu cirewa kuma da an yi ta ka ce na ce a kansa.
Na Uku: Daga baya al'amarin ya bayyanar da kunyata Mu'awuya wanda bai yi aiki da ka'idojin sulhun ba ko kadan sa'an nan kuma an gano babbar gudummawar da Imam Husain (A.S.) ya kaddamar da sadaukar da kan da ya yi cewa cikato ne na gudummawar Imam Hasan wajen fuskantar azzalumai da fuskantan fandarewa.
Na Hudu: Imam Hasan (A.S.) ya yi aiki da abinda ya zo na daga sunna da salon rayuwar Annabi (S.A.W.A) yana mai koyi da shi, domin ya yi kokarin shiryarwa zuwa ga sakon, sai aka fuskance shi da wannan matsayin, kuma ya rike a matakinsa da kuma kafa hujja da shi daga matsayin Sulhun Hudaibiya.
Na Biyar: Sulhun shi ne kawai abin koyi guda daya wanda Imaman Ahlul Bait (A.S.) suka tsara Siyasarsu ta hikima da shi domin Imam Hasan (A.S.) ya aza nakiya ce a hanyar Mu'awuya da shi wanda zai tarwatsa shi ta yadda bai sani ba, kuma ya sanya sunnar ruguza fadar Umayyawa ta hannun su Umayyawan da kansu.
Tarihi ya kawo cewa Mu'awuya ya karya alkawarin Sulhun da ya yi bayan sojojin Kufa sun koma gare shi yayin da ya tashi yana magana yana cewa:
"Ya ku mutanen Irak -ni- wallahi ban yake ku domin ku yi salla, kuma ba don ku yi azumi ba, kuma ba don ku yi zakka ba, ba don ku yi hajji ba, ni dai na yake ku ne kawai domin zama shugaba a kanku, kuma Allah Ya ba ni wannan alhali ku ba kwason haka ku ji ku sani duk abinda na bayar da shi ga Hasan Bin Ali to na take shi a karkashin kafofina biyu wadannan." Kamar yadda Ibin Asakir ya kawao a Littafin Mukhtasaru Tarikh Dimashk- Yayin da aka game mubaya'a ga Mu'awuya ya tashi ya yi jawabi ya zagi Aliyu ya zagi Hasan- har zuwa karshe karshen abinda ya auko daga manyan al'amuran da suka auku.
Sidi Abdul Husain Sharafuddin (R.A.) ya ambata cewa Imam Hasan da Imam Husain (A.S.) sun kasance kusurwoyi biyu ne na sako guda kowace kusurwa daga cikinsu tana gurinta da ya dace, a lokaci daga marhalolinsa daya na taimakon guda a kan yunkurinsa da kariyarsa yana taya shi da sadaukar da kansa a tafarkinsa...
Ranar Sabit (sulhun Hasan) ita ce mafi sananniyar ma'anar sadaukar da kai fiye da ranar Tif (Ranar Karbala) ga ma'abuta hankali ga wanda ya zarfata, Shahadar Karbala ta Hasan ce a karo na farko sa'an nan ta Husaini a karo na biyu domin Hasan shi ne ya tandi sakamakonta ya shirya musabbabanta.
Mutane sun tsaya bayan aukuwa al'amari Sibat da na Karbala suna nazarin al'amura suna ganin cewa Umayyawa wata jama'a ce ta Jahiliyya.
A duba Littafan Sulhun Hasan na Shaikh Radhi Ala Yasin, da kuma Majalisul Fakhira Fi Ma'tami Itrati Tahira, da Sharhin Nahjul Balagha Juzu'i na 4, da Imamul Hasan da Husain na Malam Abdul Ala yili, Mukhtasaul Tarikh Dimashk Juzu'i na 25 shafi na 162, da Al- Kamil Fit Tarikhul Islam na Zahabi Juzu' i na 4 shafi na 5 da Tarikhul Khulafa' (Al- Imama Was Siyasa) na Ibn Kutaiba Juzu'i na 1 shafi na 164.
Amali na Saduk na 277, da Wasa'ilus Shia Juzu'i na 16 shafi 220 hadisi na 21406.