Akidarmu Game da Aiki a Hukuma Azzaluma

Idan har taimakekeniya da azzalumai daidai da rabin dibino, kai hatta ma son wanzuwarsu na daga cikin abubuwa masu tsanani da Imamai (A.S.) suka yi gargadi game da su to mene ne kuma halin tarayya da su a cikin hukunci da kuma shiga cikin aikinsu tare da su da amintuwa da jagorancinsu?

Yaya halin wanda ya kasance daga cikin wadanda suka assasa musu hukumarsu, ko kuma wanda ya kasance daga cikin wadanda su rukunan shugabacinsu ne wadanda suka dulmuye cikin karfafa hukuncinsu, "kuma wannan saboda karbar shugabancin azzalumi rusa gaskiya ne dukkaninta kuma raya karya ne dukkaninta kuma bayyana zalunci ne da ja'irci da fasadi.[1] Kamar yadda ya zo a hadisi a "Tuhful Ukul" daga Imam Sadik (A.S.)

Sai dai kuma ya zo daga gare su (A.S.) halaccin yarda da Shugabancin Ja'irai idan a ciki akwai kiyaye adalci, da tsayar da haddin Allah da kyautatawa ga muminai, da yin umarni da mai kyau da hana ayyuka munana, "A kofofin azzalumai Allah na da wadanda Allah Ya haskaka su da hujjoji, Ya ba su iko a kasashe, kuma Yana kare waliyanSa da su, kuma Yana gyara al'amuran musulmi da su... Su wadannan muminai ne na hakika su wadannan manarorin Allah ne a bayan kasa wadannan hasken Allah ne a cikin ababan kiwonsa..." kamar yadda ya zo a hadisi daga Imam Musa Bin Ja'afar[2] (A.S.)

A wannan Babin akwai hadisai da dama, wadanda ke bayyana tafarkin da ya kamata shugabanni da masu aiki ya kamata su tafi a kai, kamar abinda ya zo a wasikar Imam Sadik (A.S.) ga Najjasi Shugaban Ahwaz (A duba Al- Wasa'il Kitabul Bay'i Babi na 78.[3]


[1] Tuhful Ukul hadisi na 332.

[2] Biharul Anwar Juzu'i na 75 shafi na 38 Hadisi na 46 daga Munyatul Murid, a cikinsa akwai hadisi daga Imam Ridha (a.s.).

[3] A duba Wasa'ilus Shi'a Juzu'i na 17 shafi na 196 hadisi na 22338 da sauran hadisan Babi na 36 daga babobin "Maktusiba bi kashfar Rayba." 86.