Imaman Ahlul Bait (A.S.) babu wata himma da
suka kasance da ita bayan sun kawar da kansu daga sa ran dawowar al'amarin
al'umma gare su face himmar gyara musulmi da tarbiyyantar da su tarbiyyar da ta
dace kamar yadda Allah Ta'ala yake so daga gare su. Don haka su kasance tare da
duk wani da yake bin su kuma suka hakikance da rashin tona asirinsu suna
matukar kokarinsu wajen koya masa hukunce-hukuncen Shari'a, suna cusa masa
ilimin Muhammadiyya, suna sanar da shi abinda yake nasa da kuma wanda yake
kansa.
Ba sa daukar mutum
cewa mabiyansu ne, daga Shi'awansu ne sai dai idan ya kasance mai bin Allah,
mai nesantar son zuciyarsa mai riko da koyarwarsu da shiryarwarsu.
Ba su daukar cewa soyayya gare su kawai ta
wadatar wajen tsira, kamar yadda wasu ke gamsar da kansu daga cikin masu kage
da bin sha'awace - sha'awace, kuma wadanda ke neman uzurin kangarewa biyayya ga
Allah su Imamai, ba sa daukar soyayya gare su da biyayya ga shugabancinsu tsira
ne sai dai idan an hada da kyawawan ayyuka, an kuma yi halin biyayya gare su da
gaskiya da rikon amana, da tsoron Allah da takawa.
"Ya
Khaisama ka isar ga mabiyanmu[1]cewa ba za mu dauke masu komai ba daga
Allah face da aiki, kuma su ba za su samu soyayyarmu ba sai da tsoron Allah,
kuma lalle mafi hasarar mutane ranar Alkiyama shi ne wanda ya siffanta adalci
sannan kuma ya saba masa zuwa wani abu da ba shi ba."2
Sai dai su suna son mabiyansu ne su zamanto
masu kira zuwa ga gaskiya, masu shiryarwa zuwa ga alheri da rabonta kuma suna
ganin cewa kira a aikace ya fi kira da harshe isarwa "Ku kasance masu
kiran mutane zuwa ga alheri ba da harsunanku ba, su ga kokari da gaskiya da
tsoron Allah daga gare[3]ku.
A halin yanzu za mu kawo maka wata muhawara da
ta gudana tsakaninsu da wasu daga cikin mabiyansu domin ka san tsananin
himmatuwarsu da kwadayinsu a kan gyara dabi'un mutane:
1-
Muhawarar Abu Ja'afar Bakir (A.S.) da Jabir Ja'afi:
"Ya
Jabir ashe wanda yake sanya wa kansa cewa shi Shi'a ne zai wadantu kawai da
soyayya gare mu mu Ahlul Bait? To wallahi babu wani Shi'a mai bin mu sai dai
wanda yaji tsoron Allah ya bi Shi."
Su ba a kasance an
san su ba sai da kankan da kai da tsoron Allah, da amana da yawan zikirin
Allah, da azumi, da salla, da bin iyaye, da alkawari ga makwabta fakirai da
matalauta da mabarsa da marayu tare kuma da gaskiyar magana da karatun
Alkur'ani da kame harshe daga ambaton mutane sai dai da alheri, kuma sun
kasance aminan jama'arsu a kan al'amura.
Saboda haka ku ji tsoron Allah kuma ku yi aiki
saboda abinda yake ga Allah, babu wata dangantaka tsakanin Allah da wani, mafi
samun soyayya a gurin Allah a cikin bayi shi ne mafificinsu a tsoron Allah da
kuma mafificinsu a aiki da biyayyarsa."
Ya Jabir Wallahi ba mu kusanta ga Allah sai dai
da da'a, kuma babu kubutarwa daga wuta a gare mu, kuma babu wata hujjar wani a
kan Allah, duk wanda ya kasance mai biyayya ga Allah to shi masoyi ne gare mu
duk wanda ya kasance mai sabo ne ga Allah to shi makiyi ne gare mu, kuma ba a
samun jagorancin mu sai da aiki da tsoron [4] Allah."
2-
Muhawarar Abu Ja'afar (A.S.) da Sa'id Bin Hasan:
Abu Ja'afar (A.S.): " Ashe dayanku zai zo
ga dan'uwansa ya iya hannunsa a jakarsa ya dauki abinda yake so bai cire shi
ba".
Sa'id: Ban san wani da haka ba a cikinmu.
Abu Ja'afar (A.S.): " To babu kome ke
nan."
Sa'id: " To halaka ke nan."
Abu Ja'afar (A.S.): " Mutane ba a ba su
mafarkinsu ba ke nan tukunna."[5]
3-
Mahawarar Abu Abdullah Sadik (A.S.) da Abi Sabahi Kanani:
Kanani ya ce ga Abi Abdullahi "Abinda muke
gamuwa da shi daga mutane game da ku."
"Menene abinda kuke gamuwa da shi daga
mutane?"
Kanani: Bai gushe
ba magana na gudana tsakaninmu da mutane ya ce dan Ja'afariyya ne mugu.
Abu Abdillahi:
"Mutane na aibata ku a kaina ?"
Kinani: E!
Abu Abdillah: Karanci mai bin Ja'afar a cikinku
ya yawaita! Sahabbaina kawai su ne wanda tsoron Allah gare Shi ya yawaita, kuma
ya yi aiki ga mahaliccinsa kuma ya tsammaci ladansa. Wadannan su ne
sahabbaina."[6]
4-
Abi Abdillah (A.S.) yana da wasu maganganu game da wannan al'amari, daga ciki
za mu kawo abinda ke biye:
a- "Baya daga cikinmu -babu karama kuma-
wanda ya kasance a cikin wani birni da adadin dubu dari ko fiya da haka, kuma
wani a cikin wannan birni ya zamanto ya fi shi tsoron Allah."[7]
b- "Mu ba ma kidaya mutum mumini har sai
ya zamanto mai biyayya ga dukkan umarninmu da kuma nufi, ku ji ku sani daga
cikin bin umarninmu da kuma nufinsa ne tsoron Allah, don haka ku zamanto kun
kawata da Shi, Allah Ya rahamshe[8] ku."
c- "Wanda mata masu tsari basu magana game
da tsanteninsa ba ya daga cikin Shi'awanmu, haka kuma wanda ya kasance a cikin
karamin gari mai adadin mutane dubu goma, daga halittun Allah daya a cikinsa ya
fi shi tsoron Allah."[9]
d- "Shi'awan Ja'afar, mabiyansa, kawai su
ne: wanda ya kame cikinsa da farjinsa kokarinsa ya tsananta, kuma ya yi aiki ga
mahaliccinsa ya sa rai da sakamakonSa kuma ya ji tsoron ukubarSa. To idan ka ga
wadannan to wadannan su ne Shi'awan Ja'afar."[10]