Addu'o'in Sahifatus Sajjadiyya


Bayan aukuwar al'amarin Karbala mai ban takaici da kuma kame ragamar shugabancin al'ummar musulmi da Banu Umayya suka yi kuma suka dulmuya a cikin danniya, suka yi dumu-dumu da jinin mutane, sa'an nan suka yi watsi da koyarwar addini sai Imam Zainul Abidin (A.S.) wato Sayyiddus Sajidin Ya zauna a gidansa yana bakin ciki da jin takaici. Yana gida babu wani mai kusatarsa kamar yadda ba zai iya yada wa mutane abinda ya wajaba a kansu ko ya kamata su sani ba na addini.
Don haka ala tilas ya zama babu makawa gare shi ya dauki salon addu'a wanda muka ambata da cewa yana daga cikin hanyoyin koyarwa da ladabtar da zukata ya rike shi a matsayin hanyar yada koyarwar Alkur'ani da ladubban musulunci da kuma sanar da tafarkin Ahlul Bait (A.S.) da kuma hanyar cusa wa mutane ruhin addini da zuhudu da kuma abinda ya wajaba na daga gyaran zukata da kuma kyawawan dabi'u.
Wannan hanya ce da ya fare ta a fakaice don koyar wa mutane ba tare da ya jawo hankalin azzaluman Shugabanni da ke matsa masa ba, ba kuma za su iya kafa masa wata hujja ba. Don haka ne yawancin Wadannan addu'o'i masu zurfi an tattara wadansunsu a littafin Sahifatus Sajjadiyya wanda ake yi wa lakabi da "Zaburar Zuriyar Muhammadu (S.A.W.A)" salonta da manufofinta sun zo da siga da salon Larabci mafi daukaka, da mafi ingancin asirran tauhidi da Annabci da kuma mafi ingancin hanyar koyar wa da kyawawan dabi'u ababan yabo da kuma ladubban musulunci.
Wadannan addu'o'in sun shafi al'amura dabam-daban ne na tarbiyya ta addini ta shafi koyarwar addini da kyawawan dabi'u ta hanyar addu'a, ko kuma addu'a ce amma da salon koyar da addini da kuma kyawawan dabi'u. Alal hakika bayan Alkur'ani da Littafin Nahjul Balagha wannan Littafin addu'o'in shi ne salon bayanin Larabci mafifici kuma mafi daukakar mashayar manufar sanin Ubangiji da kyawawan dabi'u. Daga cikinsu akwai wanda ke sanar da kai yadda zaka daukaka Allah kuma ka tsarkake Shi, kana kuma ka yi hamdala ka yi wa Allah godiya, daga bisani ka tuba gareShi.
Daga ciki akwai wadda ke sanar da kai yadda zaka yi zance da Allah, kuma ka kadaita da kai ga Ubangijinka kana mai bayyana Masa asirinka sannan ka zabura zuwa gare Shi.
Daga cikinta akwai wadanda ke shimfida maka ma'anar Salati ga Annabi (S.A.W.A) da Manzannin Allah da zababbunSa daga cikin halittunSa da yadda za ka yi da Shi.
Daga cikinsu akwai wadanda za su fahimtar da kai abinda ya dace ka bi iyayenka da shi.
Kazalika akwai wadanda ke maka sharhin hakkokin Uba a kan dansa, ko kuma hakkokin makwantai, ko wadanda kuke ciki daya, ko hakkokin musulmi baki daya, ko hakkokin matalauta a kan mawadata da kuma akasin haka.
Daga cikin addu'o'in akwai wanda zai fadakar da kai kan abinda ya wajaba na basussukan mutane akan ka, da kuma abinda ya kamata ka aikata akan lamurran kafi da tattalinsu, haka na da abinda ya kamata kayi mu'amala da shi tsakaninka da masu hulda da sauran abokanka da kuma mutane baki daya, har yanzu akwai wanda zai gwada maka irin mutanen da za ka iya hulda da su domin amfanin kan ka.
Daga cikinsu akwai wadanda suke hado maka dukkan manyan halayen kwarai da za sa su iya zama cikakken tsari na ilimin kyautata dabi'u.
Daga cikinsu akwai wadanda za su koya maka yadda za ka yi hakuri a kan munanan abubuwa da ke aukuwa da kuma yadda za ka yi yayin da kake ciwo da kuma yayin da kake kalau.
Daga cikinsu akwai wadanda ke maka sharhin wajiban sojojin musulunci da wajiban mutane dangane da su... da dai sauran wadannan da kyawawan dabi'u abin yabo suke farlanta su, duk ta hanyar addu'a kawai.
Bayyanannun al'amuran da ke fitowa fili a addu'o'in Imam sun kasu kamar haka:- Na farko:
Sanin Allah Ta'ala da girman kudurarSa da bayanin kadaita Shi, da tsarkake Shi, da mafi dacewar ma'anoni na ilimi, wannan kuwa yana maimaituwa ne a kowace addu'a ta salo dabam-daban kamar yadda kake karantawa a addu'a ta farko:
"Godiya ta tabbata ga Allah na farko wanda babu wani na farko da Ya kasance kafin Shi, Na karshen da babu wani na karshe da zai kasance baicin Shi Wanda idandunan masu gani suka gaza ganinSa, wahamce - wahamcen masu sifance - sifance kuma suka gajiya wajen siffanta Shi. Ya fari halittu da kudurarSa a farkon farawa Ya kuma kago su kamar yadda Ya so kagowa."
Karanta ma'ana ta farko da kyau kuma ka yi tunani a kanta za ka tsarkake Allah Ta'ala daga kasancewarSa wani ya zamanto ya gewaye da gani ko da wahami, da kuma ginin ingancin ma'anar halitta da kuma halittar duniya baki daya.
Daga nan kuma ka karanta wani salon wajen bayyana kudurar Allah Ta'ala da yin tuntuni a addu'a ta 6:
"Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya halitta dare da rana da karfinSa, Ya rarrabe tsakaninsu da kudurarSa, Ya sanya ga kowane daga cikinsu su biyun iyaka ayyananniya, Yana shigar da kowane daya daga cikinsu a cikin dan'uwansa a cikinsa da kaddarawarsa ga bayi a cikin abinda yake ciyar da su kuma Yake sanya su su girma. Don haka Ya halitta musu dare ne domin su huta wahalar kaiwa da komowa da dawainiya kuma Ya sanya shi sutura da za su suturtu da kwanciyarsu da natsuwarsa domin hakan ya zama musu wartsakewa da kara samun karfi kuma domin su kara samun jin dadi da sha'awa."6 Har zuwa karshen abubuwan da ya ambata na fa'idar halittar rana da dare da kuma abinda ya kamata mutum ya yi godiyarsa daga wannan ni'imar.
A wani salon kuma na bayanin dukkan al'amura ga Allah Ta'ala suke za ka karanta a addu'a ta 7 cewa:
"Ya wanda da Shi ne kulle-kullen munanan abubuwa ke suncewa, Ya wanda da shi ne kaifin tsanani ke duskurewa, Ya wanda daga gare Shi ake rokon mafita zuwa tsantsan sauki mawuyatan al'amura na rusunawa ga kudurarKa, sabubba kuma sun samu ne da tausasawarKa, kaddarawarKa kuma ta gudana ne a bisa iradarKa, su da iradarKa suke bin umarninKa, kuma masu umartuwa da maganarKa ne kuma da iradarKa ne suke tsawatuwa da haninKa."

Na Biyu:

Bayani game da falalar Allah ga bawanSa, da kuma gazawar bawa wajen bayar da hakkin Allah Ta'ala kome abinda ya yi na da'a da ibada kuwa da kuma yankuwa don juyawa ga Allah kamar yadda kake karantawa a addu'a ta 37:
Ya Allah lalle babu wani da zai kai ga matukar godiya gare Ka face wata kyautatawarKa ta same shi wadda za ta sake lizimta masa wata godiyar. Kuma ba ya kaiwa ga matukar da'arKa koda kuwa ya dage face ya gaza yin yadda Ka cancanta a kan falalarKa, Mafificin mai godiya gare Ka a bayinka ya gaza a kan godiyarKa, kuma mafi bautarsu mai kwauro ne a bautarKa."
Saboda girman ni'imomin Allah Ta'ala a kan bawanSa bawan ya yi kadan ya ba da hakkinSa komai kokarin da ya yi kuwa.
To yaya kuma idan har ya sabe Shi yana mai tsaurin kai, yayin nan kuma ba zai taba iya kankare sabo koda guda daya ba, kuma wannan shi ne abinda yankin addu'ar da ke biye a addu'a ta 16 ke nunawa:
"Ya Ubangijina idan da zan yi kuka har fatar idona ta zagwanye, kuma na yi kururuwa har muryata ta dushe, kuma na tsaya gare Ka har kafafuwana su tsattsage kuma na yi maka sujada har kwayar idandunana su faffado, kuma na ci turbayar kasa duk tsawon rayuwata kuma na sha ruwan toka har zuwa karshen zamanina sa'an nan na yi ta ambaton ka duk tsawon wannan lokacin har sai harshena ya gaza, sa'an nan kuma na zama ban taba daga ganina na dubi sama ba don jin kunyar ka, duk wannan ba zai wajabta shafe mini mummunan aiki daya daga miyagun ayyukana ba."

Na uku:

Sanar da lada da ukuba da aljanna da wuta da kuma cewa ladan Allah dukkaninsa kyauta ce kawai kuma bawa ya cancanci azaba ne da zarar aikata sabo guda daya kawai da ya yi tsaurin idon aikatawa, Kuma Allah na da hujja a kansa game da haka.
Kuma dukkan addu'o'in Sahifatus Sajjaddiya na ambata wannan ukubar mai tasiri domin samar wa zuciya tsoron ukubar Allah Ta'ala da sanya mata sa tsammani da ladan Allah Ta'ala. Dukkanta shaida ce a kan haka ta salo mafifici da ke sa wa zuciya mai tuntuni tsoro da firgita kan kama hanyar sabo, wato kamar abinda za ka karanta a addu'a ta 46:
Hujjarka tabatacciya ce ba za ta shafu ba, Shugabancinka tsayayye ne ba ya ciruwa, don haka tsananin azaba madawwami ya tabbata ga wanda ya nesance Ka, tabewar tozartuwa ta tabbata ga wanda ya karkace daga gare Ka, tsiyacewar tsiyata ta tabbata ga wanda ya rudu ya bar Ka, jujjuyawarsa a azabarKa ta yawaita, taraddudinsa a cikin ukubarKa ya yawaita, bukatarsa ga samun budi ta kai matuka, debe tsammaninsa ga samun mafita mai sauki ya tsawaita, Adalci ne daga hukuncinKa ba Ka zalunci a cikinsa, da kuma yin daidai a hukuncinKa ba ya kaucewa, lalle Ka bayyanar da hujjoji kuma Ka jarraba uzurori."
Da kuma kamar yadda kake karantawa a addu'a ta 31.
"Ya Allah Kaji kan kadaitakata a gaban Ka, da kidimewar zuciyata daga tsoronKa da firgicewar gabobina don haibarKa, kuma lalle Ya Ubangijina zunubina ya sanya ni a matsayin kaskanci a gurinKa. Idan har na yi shiru babu wani da zai yi magana a madadina, idan kuma na nemi a cece ni to ni ban cancanci ceto ba."
Da kuma wadda kake karantawa a addu'a ta 39:
"Domin Kai idan har Ka saka mini daidai wadaida to za Ka halakar da ni. Idan kuma ba Ka lullube ni da rahamarKa ba to za Ka halakar da ni. Kuma ina rokon Ka Ka dauke daga zunubina wanda nauyinsa ya dankare ni. Kuma ina neman taimako da kai a kan abinda nauyinsa ya riga ya makure ni. Don haka Ka yi dadin tsira ga Muhammadu da zuriyarsa. Kuma Ka ba wa raina kansa saboda zaluncinsa ga ni kaina, kuma Ka wakilta rahamarKa wajen daukar nauyina."

Na Hudu:


Jan mai addu'a zuwa ga madaukakan matsayin ayyuka da kebantattun siffofi domin kyautata ruhinsa da tsarkake zuciyarsa ta hanyar karanta wannan addu'ar kamar yadda kake karantawa a addu'a ta 20:
"Ya Allah Ka kammala min niyyata da tausasaawarKa, kuma Ka inganta mini niyyata da abinda ke gare Ka, kuma Ka gyara mini abinda ya baci daga gare ni da kudurarKa, ...Ya Allah Ka yi dadin tsira ga Muhammadu da zuriyar Muhammadu Ka jiyar mini dadi daga shiriya ingantacciya wadda ba zan taba neman musayenta ba, da kuma hanya ta gaskiya wadda ba zan taba karkacewa daga kanta ba, da kuma niyyar shiriya daba zan taba kokwanto a kanta ba.
... Ya Allah Kada Ka bar wani hali da yake aibi gare ni face Ka gyare shi, ko kuma wani laifi da za a zarge ni da shi illa Ka kyautata shi. Ko kuma wani halin karimci da yake tauyayye gare ni har sai Ka cika Shi."

Na Biyar:

Sanya wa mai karanta addu'ar mutumta mutane da rashin kaskantar da su, da kuma cewa kada ya sanya bukatarsa a gurin wani ba Allah ba da kuma cewa kwadayin abinda ke hannun mutane na daga cikin mafi kaskancin abinda mutum zai siffantu da shi kamar yadda kake karantawa a addu'a ta 20:
"Kuma kada Ka fitine ni da neman taimakon wani ba Kai ba idan na matsu da kuma kankan da kai don tambayar wani ba Kai ba idan na bukata, da kuma mika wuya gaba ga wanda ba Kai ba idan na tsorata, kada na zamanto na tozarta da hanawa da kau da kai ta yin haka."

Da kuma misalin addu'a ta 28:

"Ya Allah ni na tsarkake niyyata gare Ka duka, kuma na juyo zuwa gare Ka baki daya, kuma na juyar da fuskata daga dukkan ma'abucin taimakonKa, Na juyo da al'amarina daga dukkan wanda ba zai taba wadatuwa ya bar falalarKa ba, kuma na gane cewa bukatar mabukaci zuwa ga wani mabukacin wautar ra'ayinsa ne kuma bacewar hankalinsa ne."

Kazalika addu'a ta 13:

" Duk wanda ya yi kokarin magance rashinsa ta gurinKa kuma ya yi kokarin raba kansa da talauci da taimakonKa to lalle ya nemi abin bukatarsa a gurin da ake tsammani, kuma ya zo wa bukatarsa ta gurin da ya dace. Kuma duk wanda ya juya da bukatarsa zuwa ga daya daga cikin halittunKa, ko kuma ya sanya shi sababin cim mata ba kai ba , to lalle ya jawo wa kansa hani kuma ya cancanci kubucewar kyautatuwa daga gare Ka."

Na Shida:

Koya wa mutane wajabcin kiyaye hakkokin wasu, da taimaka musu da tausasawa gare su, da rangwame ga junansu, da sadaukarwa da tabbatar da ma'anar 'yan'uwantakar musulunci, kamar yadda kake karantawa a

addu'a ta 38:

" Ya Allah ni ina mai neman uzuri daga gare Ka a kan dukkan wani da aka zalunta a gabana amma ban taimake shi ba, da kuma wani kyakkawan abu da aka kwararo mini shi amma ban yi godiyarsa ba da kuma duk wani mabukaci da ya roke ni amma ban ba shi ba, da kuma daga hakkin duk wani ma'abucin hakki da ya hau kaina daga muminai amma ban cika mashi ba, da kuma daga dukkan wani aibi na mumini da ya bayyana gare ni amma ban suturce shi ba. "
Lalle wannan irin neman uzuri yana daga cikin mafi bayyanar abinda zai fadakar da zuciya zuwa ga abinda aikata shi ya kamata na wadannan kyawawan dabi'u madaukaka da Ubangiji Ya yarda da su.
A addu'a ta 39 akwai abinda ke bada karin haske a kan haka tare da lizimtar da kai yadda za ka yafe wa wanda ya munana maka yana kuma gargadinka game da yin ramuwar gayya yana kuma daukaka zuciyarka zuwa matsayin tsarkakuwa: "Ya Allah duk wani bawa da ya cutar da ni da wani abu da ka haramta, kuma ya keta mini abinda Ka riga Ka hane shi a kai, kuma ya mace da zaluntata ko kuma ya auku a kaina daga gare shi yana rayayye, to Ka gafarta masa abinda yayi mini, Ka yafe masa abinda ya riga ya aukar ya wuce daga gare ni, kada ka dakatar da shi da tambaya a kan abinda ya aikata a kaina, kuma kada ka tona asirinsa a kan abinda ya aikata a kaina, kuma ka sanya rangwamen da na yi masa na afuwa gare su da kuma sallamawar da na yi musu na daga sadaka gare su ya zama sadakar masu sadaka, kuma mafi kololuwar sadarwar ma'abuta kusanci gare Ka. Kuma Ka musanya mini afuwata gare su da afuwarKa, da kuma addu'ata gare su rahamarKa, har ya zamanto kowane daya daga cikinmu ya rabonta da falalarKa ya kuma samu tsira saboda baiwarKa."
Al'ajabin wannan yankin addu'ar da yawa yake, kyawun tasiri da shigarta zuciyar zababbu ya yawaita, don fadakar da su a kan lizimtar kyakkyawar niyya da dukkan mutane, da neman rabbonta ga kowa da kowa hatta ma wanda ya zalunce shi ya ketare masa haddi.