Akidarmu game da addu'a:

Manzon Allah (S.A.W.A) Ya ce: "Addu'a makamin Mumini ce, kuma jigo addini sa'an kuma hasken sammai da kasa ce."[1]

Kazalika ta zamanto daga abubuwan da shi'a suka kebantu da su na musamman kuma sun rurrubuta littafa a kan falalarta da ladubbanta kuma a addu'o'in da aka ruwaito su daga Ahlul Bait sun kai littattafa da dama, mayalwatansu da takaitattunsu. A cikin wadannan littafan akwai abubuwan da aka kawo da ke nuna cewa Annabi (S.A.W.A.) da Ahlul Bait (A.S.) suna zaburar da musulmi da kwadaitar da su ga addu'a hatta ya zo daga gare su cewa: "Ibada mafifciya ita ce addu'a.[2] Da kuma cewa:"Aikin da yake mafi soyuwa a gurin Allah shi ne addu'a."[3]

Hakaza ya zo cewa: "Lalle addu'a tana kore kaddara da bala'i."120 Da kuma cewa "Addu'a ita ce maganin dukkan cuta. "[4]

Har ila yau ya zo cewa Amirul Muminin Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) ya kasance Mutum ne ma'abucin addu'a Wato mai yawan addu'a hakan nan kuwa ya kamata ya kasance saboda kasancewarsa shi ne shugaban masu tauhidi kuma shugaban mabiya ubangiji. Addu'o'insu sun zama tamkar hudubobinsa a matsayin ayoyi daga fasahar Larabci ne kamar shahararriyar addu'ar Kumail Bin Ziyad[5] wadda ta kunshi ilimin sanin ubangiji fuskantarwar addini da kuma abinda ya dace ya zamanto madaukakin tafarki ga sahihin musulmi.

Alal hakika lalle addu'o'in da aka kawo daga Annabi (S.A.W.A) da Ahlul Bait (A.S.) su ne mafificin tsarin rayuwa ga musulmi idan ya yi tuntuntuni a kansu, sukan cusa masa karfin imani da karfin akida da ruhin sadaukar da kai a kan gaskiya, kuma tana sanar da shi sirrin ibada da dadin Zance da Allah Ta'ala da yankewa daga kome zuwa gare shi, da kuma cusa masa abinda ya wajaba a kan mutum ya aikata ga Allah Ta'ala sosai; ya kuma nesanta shi daga barna da son rai da bidi'a da bata.

A takaice dai wadannan addu'o'in takaitacciyar sani ne na addini ta fuskar kyawawan dabi'u da gyara zukata da kuma nahiyar akidar Musulunci bil hasali ma dai ita tana daga cikin muhimman madogarar ra'ayoyin falsafa, da binciken ilimi dangane da sanin ubangiji da kyawawan dabi'u.

Idan da mutane sun iya - kuma ba dukansu ne masu iyawa ba,- da sun shiriya da shiryarwar da wadannan addu'o'in ke tasowa da ita a cikin madaukakin abinda ta kunsa to da ba za ka sami irin wannan fasadin da kasa ke cike da ita ba. Kuma da wadannan rayukan da sharri ya daure su, da sun yi shawagi a sammai na Allah Ta'ala cikin `yanci da walwala.

Saidai ina ma dan Adam zai samu ya saurari kalmar salihai da masu kira zuwa ga gaskiya. Hakika fadar Allah a wannan aya ta bayyana hakikanin mutane inda Allah ke cewa:

"Lallai zuciya tabbas mai umarni da mummuna ce." Surar Yusuf: 53.

"Kuma yawancin mutane ba masu shiryuwa ba ne ko da kayi kwadayi". Surar Yusufi: 103.

Na'am lalle kankamar mummunan aiki a zuciyar mutum shi ne rudin kansa da kansa da jahiltar mumumunan aikinsa da gangan da yaudarar kansa cewa shi yana aikata kyakkyawan aiki ne, don haka yake zalunci yana ketare iyaka, ya yi karya, ya yi kage, ya bi sha'awarsa yadda ransa yake so, amma tare da haka yana yaudarar kansa da cewa shi bai yi kome ba face abinda ya dace ya aikata, ko kuma ya runtse da gangan a kan mummunan da ya aikata yana kuma kaskantar da kuskurensa da kansa.

Su wadannan addu'o'in daga hadisai da ke samun karfafa daga tushen wahayi suna kokari ne su sa mutum ya koyi zargin kansa, ya juya ga Allah Ta'ala, domin su cusa masa ikrari da kuskurensa da kuma cewa shi mai aikata zunubi ne wanda ya wajaba a kansa ya katse kome ya juya ga Allah Ta'la domin neman tuba da gafara; kuma domin ya shafe guraren rudi da na laifi a zuciyarsa, wato kamar misali ya ce yana mai addu'a daga cikin Addu'ar Kumail:

"Ya Ubangijina, Ya Majibincina, ashe Za ka gudanar da hukunci a kaina a kan abinda na bi son raina a cikinsa, kuma ban kiyaye kawatawar abokin gabata ba a cikinsa, don haka ya rude ni da abinda ya so, kuma hukuncinKa ya taimake shi a kan haka, har na ketare wasu daga cikin dokokinKa da abinda ya gudana gare ni na daga haka, kuma na saba wa wasun umarce-umarcenKa."[6]

Babu shakka cewa misalin irin wannan ikrarin a cikin kadaici ya fi sauki ga mutum a kan ikarari a cikin jama'a koda kuwa yana daga cikin mafi tsanani halaye a kan zuciya kawai, idan kuwa tsakaninsa da kansa daga shi sai shi a kadaice, kuma idan hakan ya tabbata ga mutum to lalle yana da al'amari mai girma wajen rangwamta

zurfafawar zuciyarsa masharraciya da kuma horar da ita a kan neman alheri.

Duk wanda yake son tarbiyyar zuciyarsa to babu makawa ya koyar da ita kadaitaka da `yantaccen tunanin domin yi mata hisabi, kuma mafificiyar hanyar wannan kadaitakar da yi wa kai hisabin shi ne mutum ya dukufa a kan karanta wadannan addu'o'in da aka samo daga ruwayoyi wadanda ke ratsa zuciya da abinda ta kunsa, alal misali kamar ya karanta addu'ar Abi Hamza Simali (R.A.)[7]

"Ya Ubangiji Ka rufe ni da suturcewarKa, Ka yafe mini zargina da girman fuskarKa."

Yi tunani a kan wannan kalma, "Ka rufe ni" a cikinta akwai abinda ke tayar wa zuciya kwadayin suturce abinda ta tattara a kai na daga mummunan aiki, domin mutum ya fadaka, a kan wannan sashen na kunshe wanda kuma zai san haka idan ya karanta wannan addu'ar da ke biye daga bisani.

"Idan da yau wani baicin Kai ya san da zunubina to da ban aikata ba kuma da na tsoraci gaggauta ukuba da na nesanci zunubin".

Wannan irin ikrari daga cikin zuciya da kuma fadaka zuwa ga kwadayin suturce abinda yake da shi na daga munana yana tayar da kwadayin neman gafara da yafewa daga Allah Ta'ala don gudun kada ya tozarta shi a gurin mutane idan da Allah Ya so Ya yi masa ukuba a nan duniya ko kuma a lahira a kan ayyukansa, to mutum sai ya dandani dadin addu'ar asiri da zance da Allah a asirce, ya yanke ya koma ga Allah Ta'ala, ya yi godiya gare Shi, da Ya yi masa afuwa baicin Yana da kudura amma Bai fallasa shi ba yayin da yake cewa a addu'a bayan abinda ya gabata:

"To godiya ta tabbata gare Ka akan hakurinKa bayan saninKa da yafewarKa bayan kudurarKa."[8]

Sa'an nan kuma addu'ar ta sake biyar da ainihin wannan tafarkin na neman uzuri ga zuciya a kan abinda ta yi sakaci dangane da shi saboda wannan afuwa da hakuri daga gare Shi Allah Ta'ala, domin sadarwa tsakanin bawa da Ubangijinsa har ila yau kuma domin koya wa bawa cewa sabonsa ba wai don kafirce wa Allah ba ne ko kuma wulakanta Umarninsa yayin da yake cewa:

"Kuma hakurinKa gare ni yana dauka ta yana ja na zuwa ga saba maKa kuma suturcewarKa na kira na zuwa ga karancin jin kunya, kuma sanina game da yalwar rahamarKa da girman afuwarKa yana gaggautar da ni zuwa ga kifuwa a kan abubuwan da ka haramta."

Wannan shi ne tsarin salon addu'ar asirce ta tarbiyyantar da zukata, da sabar musu da da'a da barin aikata sabo.

Wannan littafi ba zai wadatar ba in kawo irin wadannan misalai fiye da haka kuma suna da yawan gaske amma kuma yana kayatar da ni in kawo wasu misalan addu'o'in salon kafa hujja gaba ga Allah Ta'ala domin neman afuwa da gafara kamar dai yadda kuke karantawa a addu'ar Kumail Bin Ziyad:

"Kuma kaitan sanina, Ya shugabana, Ya majibincina, ashe Ka sanya wuta a kan fuskokin da suka kifu ga girmanKa suna masu sujada, da kuma a kan harsunan da suka yi furuci da kadaitakarKa suna masu gaskiya, sannan kuma da godiyarKa suna masu yabo, da kuma a kan zukata da suka kewaye ilimi game da kai har suka zamanto masu tsoro, da kuma a kan gabobi da suka yi kokari zuwa guraren ibadarKa da son ransu, suka kuma yi ishara ga afuwarKa suna masu mika wuya? Ba haka zato yake game da Kai ba, ba kuma mune muka fi sanin falalarka ba."

Ka maimaita karanta wannan bangaren sa'annan ka yi tunani game da taushin wannan irin kafa hujjar da kololuwar fasaharsa da azancin bayaninsa. A halin tana sanya wa zuciya ikrari da kwauronta a ibada har ila yau kuma tana cusa mata rashin debe tsammani daga rahamar Allah da baiwarSa, sa'annan kuma tana yi wa zuciya magana da zance irin na tausasawa wani bangare a boye domin ya cusa mata madaukakan wajibanta, domin tana kaddara cewa ita dama ta riga ta ba da wadannan wajibai baki daya. Sa'an nan kuma tana koya wa mutum cewa da wadannan ayyukan ya cancanci fifitawa daga Allah ta hanyar gafartawa, wannan kuwa wani abu ne da kan zaburar da mutum ya koma ga zuciyarsa don ya aikata abinda ya wajaba a kansa ya aikata idan har bai aikata shi ba.

Karanta wani salon addu'ar da a ke neman uzuri a ci gaba da wannan addu'ar har wa yau: "To Ka sani ina iya hakuri Ya ubangijina Ya shugabana majibincina a kan azabarKa amma ta yaya zan yi hakuri a kan rabuwa da Kai, kuma ko da na iya hakuri a kan zafin wutarKa amma yaya zani yi hakuri a kan rashin dubi zuwa ga girmanKa."

Wannan wani irin cusa wa zuciya jin dadin samun kusanci ga Allah Ta'ala da halartar karamcinsa, da kudurarsa ne don soyayya gare shi da kuma cewa wannan irinn jin dadin ya kamata ne ya kai ga darajar da tasirinta da ta bari a kan zuciya ya fi azaba da zafin wuta girma. Idan muka kaddara cewa mutum na iya jure zafin wuta to da ba zai iya hakuri a kari waccan rabuwar ba kamar kuma yadda daga wannan bangaren addu'ar za a fahimci cewa wannan soyayyar da jin dadin na kusaci da abin kauna, abin bauta shi ne mafificin mai ceto ga mai zunubi a gurin Allah yadda Zai yafe Ya shafe masa.

Wannan dadin salo ba zai buya ba daga jin mamaki da kankan da kai ga Mai girma, Mai Hakuri, Mai karbar tuba, Mai gafarta zunubi.

Babu Laifi mu rufe wannan bayani da kawo takaitacciyar addu'a da ta kunshi kyawawan dabi'u da kuma abinda ya kamata kowane yanki na mutum da kuma nau'insa ya kamata ya siffantu da su na daga siffofi ababan yabo:

"Ya Allah Ka arzuta mu da muwafakar da'a da nesantar sabo, da gaskiyar niyya, da sanin abubuwa masu alfarma kuma Ka girmama mu da shiriya da tsayuwa daidai da daidaita harsunanmu da daidaito da hikima Ka cika zukatanmu da ilimi da sani, Ka tsarkake cikkunanmu daga haramiya, da kuma gauraye-gauraye, Ka kame hannauwanmu daga zalunci da sata, Ka runtsar da idandunanmu daga fajirci da ha'inci, Ka toshe kunnuwanmu daga jin hululu da giba, kuma Ka yi falala ga malamanmu da zuhudu da nasiha, ga masu neman ilimi kuma da kokari da shauki, ga masu sauraro kuma da biyayya da wa'aztuwa. Ga marasa lafiyar musulmi kuma da waraka da hutawa, ga matasansu kuma da rangwame da rahama.

Ga tsofaffinmu kuma da natsuwa da kwanciyar hankali, ga matasanmu kuma da komowa da yawan tuba ga matanmu kuma da jin kunya da kamewa, ga mawadatanmu kuma da kankan da kai da yalwatawa, ga matalauta kuma da hakuri da wadar zuci.

Ga mayaka kuma da cin nasara da galaba, ga kamanmun yaki kuma da kubuta da hutawa, ga shugabanni kuma da adalci da tausayawa, ga makiyaya kuma da yin daidai da kyawun hali.

Ka sanya albarka ga mahajjata da masu ziyara a guzuri da ciyarwa. kuma Ka hukunta abinda Ka wajabta masu na daga Hajji da Umara. Don falalarKa da rahamarKa, Ya mafi rahamar masu rahama."[9]

Kuma ni ina mai wasiyya ga 'Yan'uwana masu karatu da cewa kada damar karanta wannan addu'a ta kubuce musu, tare da sharadin yin tuntuntuni a kan ma'anoninta da abubuwan da take nufi tare da halarto da zuciya da fuskantowa da juyowa ga Allah da tsoro da kankan da kai da kuma karanta ta tamkar daga shiftarsa take domin bayyana kansa da ita, tare kuma da bin ladubban da aka ambata mata daga Ahlul Bait (A.S.). Domin karanta ta ba tare da fuskantar da zuciya ba to zakin baki ne kawai kuma ba ya kara wa mutum sani, ba ya sama masa kusaci, kuma ba a yaye masa tsanani ba a amsa masa addu'a da shi.

"Lalle Allah Mai girma da buwaya ba Ya amsa addu'a daga zuciya dulmiyayyiya, don haka idan kuka yi addu'a ku yi da fuskantowar zuciya sa'an nan ku jicewa lalle Za a amsa."


[1] Al- Kafi Juzu'i na 2 shafi na 339 hadisi na 1 .

[2] Al- Kafi Juzu'i na 2 shafi na 338 cikin hadisi na 1.

[3] Al- Kafi Juzu'i na 2 shafi na 339 hadisi na 8.

[4] Al- Kafi Juzu'i na 2 shafi na 341 hadisi na 1-8.

[5] Al- Kafi Juzu'i na 2 shafi ha 341 hadisi na 1.

[6] Addu'a ce wadda Amirul Mumini Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) ya koya wa Kumail Bin Ziyad Annakha'iy (R.A.) kuma ita ce addu'ar da ake kira addu'ar Khizru (A.S.) Kuma an sanya mata suna Addu'ar Kumail Ibin Ziyad- wanda daya ne daga cikin kebabbun Imam Ali (A.S.) da Imam Hasan (A.S.) ne wanda kuma ya ce ya karanta ta yana cikin sujada da daren rabin watan Sha'aban da daren kowace Juma'a, ko kuma sau daya a wata ko sau daya a shekara ko sau daya a rayuwa. A duba Misbahul Mutahajjid shafi na 844 da Al-Misbah na Kafami Juzu'i na 2 shafi na 282.123- Da ga Littafin Mishabul Mujtahid shafi na 844 Du'a'ul Kumail.

[7] Ita ce addu'ar da Abu Hamza Sumali ya ruwaito daga Imam Zainul Abidin (A.S.) ya ce ya kasance yana yana salla tsawon daren watan Azumi lokacin suhur sai ya karanta ta.

[8] Haka ya zo a Misbahul Mutahajjid Shafi na 582 da Al- Misbahu na Kafami Juzu'i na 2 shafi na 345.

[9] Al- Baladul Amin shafi na 349.