Abinda Mazhabar Ja'afariyya -Imamiyya take kai-
tare da riko da abinda ya zo daga Ahlul Bait (A.S.) Shi ne cewa Allah Ta'ala
zai komo da wasu mutane daga cikin wadanda suka mutu zuwa duniya a bisa
kamanninsu da suka kasance a kai, Zai daukaka wasu kana kuma Zai kaskantar da
wasu, kana Zai rarrabe masu gaskiya daga cikinsu daga marasa gaskiya, da
wadanda aka zalunta daga azzalumai, wannan zai auku ne bayan bayyanar Mahadi
daga zuriyar gidan Manzon Allah mafifita (tsira da aminci su tabbata a gare
su).
Ba mai dawowa sai wanda darajarsa ta imani
ta daukaka, ko kuma wanda ya kai kololuwa a barna. Bayan nan kuma sai a mutu
daga nan kuma sai zuwa tashin Alkiyama zuwa ga abinda suka cancance shi na
kyakkyawan sakamako ko kuwa ukuba, kamar yadda Allah Ta'ala Ya kawo a cikin
Alkur'ani mai girma game da burin da wadanda suka komo din ke yi, wato wadanda
ba su gyaru ba da komowarsu, don haka suka sami ukubar Allah kan cewa a dawo da
su zuwa na uku ko sa gyaru;
"Suka ce Ya Ubangijinmu Ka matar da
mu sau biyu kuma Ka rayar da mu sau biyu to mun yi ikrari da zunubanmu shin
akwai wata hanyar fita." Surar Mumin: 11.
Na'am Alkur'ani ya zo da yiwuwar komowa
zuwa duniya, hadisai da dama kuma daga Ahlul Bait (A.S.) suka zo a kan haka,
mabiya Mazhabar Ja'afariyya ko kuma Imamiyya sun yi ittifaki a kan haka sai dai
'yan kalilan daga cikinsu da suka yi tawilin abinda ya zo game da raja'a da
cewa ma'anarta ita ce komowar hukuma da Umarni da hani ga Ahlul Bait da
bayyanar Imamin da ake jira (A.S.) ba tare da komowar wasu ayyanannu ko raya
matattu ba.
Batun
raja'a kuwa a gurin Ahlus Sunna yana daga cikin abin ki wanda imani da shi ya
munana, kuma marubutansu a ilimin sanin maruwaitan hadisai suna kirga imani da
raja'a a matsayin suka ga mai ruwaya da kuma abin kiyayya gare shi wadda ke
wajabta kore ruwayarsa da watsi da ita, kuma ya bayyana cewa suna kirga ta a
matsayin karfirci da shirka, har ma ta fi muni, don haka, wannan na daga cikin
mafi girman abubuwan da suke sukan Shi'a Imamiyya da shi da kiyayya da su a
kansa.
Babu
shakka wannan duk wata mafaka ce kawai da bangarorin kungiyoyin musulunci da
can suka kasance suna riko da ita don sassansu su soki sashe da shi, kuma alal
hakika mu ba muga wani abu da zai halatta wannan mafakar ba domin imani da
raja'a ba ya soke imani da tauhidi kuma ba ya soke imani da Annabci bilhasali
ma kara inganta akidu biyun yake yi. Domin Raja'a dalili ne a kan
kudurar Allah cikakkiya tamkar dai tashin Kiyama da tayar da mamata, kuma tana
daga cikin abubuwan da suka saba wa al'ada wadanda ya inganta ta zama Mu'ujiza
ga Annabinmu Muhammadu (S.A.W.A) da zuriyar gidansa. Kuma ita raja'a tamkar mu'ujizar raya matattu ce
wadda ta kasance ga Annabi Isa (A.S.) ne sai dai ma ta fi ta cika a nan domin
wannan za ta zo ne bayan mamata sun zama rididdigaggu.
"Ya ce wane ne zai raya kasusuwa
alhali sun zama rididdigaggu. Ka ce Zai raya su Wannan da Ya fare su karon
farko kuma Shi game da dukkan halitta Masani ne." Surar Yasin: 79-87.
Amma wanda ya soki raja'a kuwa da dalilin
cewa tana daga shafewa batacciya to lalle bai fahimci bambanci tsakanin
"tanasuhi" da kuma ainihin tayar da mamata da ainihin jikinsu ba, ita
raja'a wani nau'i ne na tayar da mamata da ainihin jikinsu. Domin ma'anar
tanasuhi ita ce kauratar da rai daga wani jiki zuwa wani jikin daban da ba na
farko ba, ma'anar tayar da matattu da ainihinjikkunansu kuwa ba haka take nufi
ba, ma'anarsa ita ce komo da ainihin jikin da ainihin abubuwan ransa da suka
kebantu da shi, haka nan ma Raja'a take.
Idan
kuwa har aka ce "Raja'a" "Tanasuhi' ce to raya mamata da Annabi
Isa (A.S.) ma ya kasance yana yi "tanasuhi" ce to tayar da mamata da
komo da ainihin jikkunan mamata ma "tanasuhi" ne ke nan.
Saboda haka babu abin da ya saura illa
muhawara ta fuska biyu game da "Raja'a".
Na farko: Korarriya ce sam ba za ta auku
ba.
Ta Biyu: Karyata hadisan da suka zo game
da ita.
A bisa asasin Kaddara cewa muhawarorin
biyu daidai suke, sam yin imani da ita ba a daukar sa a matsayin kyamar da masu
adawa da Shi'a suka juya ta.
Kuma nawa ne daga cikin abubuwan da suke
daga cikin korarru wadanda sauran bangororin musulmi suka yi imani da su ko
kuma wadanda sam ingantaccen nassi bai tabbata ba game da su, amma ba su
wajabta kafirtawa da fitarwa daga Musulunci ba. Akwai Misalin su da dama, a
cikinsu akwai:
Yarda da yiyuwar rafkanuwa ga Annabi
(S.A.W.A) ko kuma aikata sabo[1] da kuma imani da Wanzuwar Alkur'anit[2]
da kuma batun "Wa'idu"[3] da kuma imani da cewa Annabi bai
ba da nassi kan halifan bayansa ba.
To
dangane da Muhawarori biyun da muka kawo a dauka cewa ba su da wani asasin
ingancin tabbatar da Raja'a amma ai mun riga
mun
bayyana cewa ita Raja'a wani nau'i ne na tayar da mamaci ko kuma komo da
ainihin jiki, sai dai kawai cewa ita tana aukuwa ne a wannan duniyar. Dalilin
kuma da ke tabbatar da yiwuwar tashin kiyama shi ne dalilin da ke tabbatar da
ita babu wani abu kuma da zai sa a yi al'ajabi game da ita sai dai kawai don
zukatanmu ba su saba da ita ba ne a rayuwanmu ta duniya, kuma ba mu da
sabubbanta da abubuwan da ke hana ta da za su sa mu yi ikrari da ita ko mu kore
ta, da kuma fahimtar cewa abu ne marar sauki ga mutum ya yarda ya gaskata
abinda bai saba da shi ba, wannan kuwa kamar wanda ya ga cewa tayar da mamata
abu ne bako ya ce: "Wanene zai tayar da kasusuwa alhali suna
rididdigaggu". Aka ce Masa:
"Wanda Ya fare su a karon farko Shine
zai raya su kuma Shi a kan komai Masani ne". (Yasin: 78-79)
Na'am a kan makamancin wannan da ba mu da
dalili na hankali akai na tabbatar da ita ko kore shi, ko kuma muka raya rashin
dalili to wannan kuwa zai kallafa mana komawa ga nassosin addini wadanda suke
daga tushen wahayin Ubangiji. Kuma abinda zai tabbatar da yiwuwar Raja'a ga
wasu matattu a duniya ya zo a Alkur'ani kamar dai Mu'ujizar Annabi Isa (A.S.) a
raya matacce: "Kuma ina warkar da wanda aka haifa makaho da kuturu kuma
ina rayar da matattu da izinin Allah." Surar Ali Imran: 49.
Da kuma fadin Allah Ta'ala: "Ta yaya
Allah Zai raya wadannan bayan mutuwarsu, sai Allah Ya matar da shi shekara dari
sa'an nan kuma Ya raya shi." Surar Bakara: 259.
Da kuma ayar da ta gabata da ke cewa:
"Suka ce Ya Ubangijinmu Ka matar da mu sau biyu." Surar Mumin: 11.
Ma'anar wannan ayar ba za ta fito daidai
ba ba tare da komowa duniya bayan mutuwa ba koda yake wasu masu tafsiri sun
wahalar da kansu wajen yin tawilin da ba zai kashe kishirwa ba kuma ba zai
tabbatar da ma'anar ayar ba.
Muhawara
ta biyu kuwa wadda ke cewa hadisai game da ita Raja'a kagaggu ne kawai wannan
da'awar ba ta da wani asasi, domin Raja'
na daga cikin al'amuran da suke ba makawa sun zo daga Ahlul Bait (A.S.) daga
hadisai masu tafarkunan ruwaya da dama.
Bayan
duk wannan ashe ba a yi mamaki ba game da mashahurin marubuci mai da'awar sani
kamar Ahmad Amin a Littafinsa na Fajrul Islam, saboda yana cewa; "Ai
Yahudanci ya bayyana a cikin Shi'anci ta hanyar batu game da raja'a[4]."
Don haka ni nake cewa gare shi:
"To
ai Yahudanci ma ya bayyana a Alkur'ani game da batun Raja'a" kamar yadda
ya gabata game da ayoyin Alkur'ani da suka ambaci raja'a.
Za
kuma mu kara masa da cewa:
Alal
hakika babu makawa Yahudanci da Nasaranci su bayyana a cikin da dama daga
abubuwan da aka yi imani da su da kuma hukunce-hukuncen musulunci, domin Annabi
Mai girma (S.A.W.A) ya zo yana mai gaskata Shari'o'i da suka gabata5
kuma koda yake an shafe wasu daga hukunce-hukuncensu. To bayyanar Yahudanci da
Nasaranci a wasu abubuwan da Musulunci ya yi imani da su ba aibu ba ne cikin
Musulunci idan ma har aka dauka cewa lalle Raja'a daga akidojin Yahudanci take
kamar yadda wannan marubucin yake da' awa.
Ko ta
halin kaka dai Raja'a ba wai tana daga cikin jiga-jigan addinin (Musulunci) da
ya wajaba a dauke ta a akida ba ne da kuma yin bincike a kanta sai dai kawai
imani da muka yi da ita biyayya ne ga hadisai ingantattu daga Ahlul Bait (A.S.)
wadanda muka yi imani da kubutarsu daga karya, kana kuma tana daga cikin
al'amuran gaibi da suka ba da labari game da ita, kuma aukuwarta ba wani abu
ban e da zai iya yiwuwa ba. Kamar yadda muka nuna wasu misalai a kan
hakan.