Ba ya halatta Imamanci ya yanke, ko ya katse a wani zamani daga zamuna5 koda kuwa Imamin a boye yake, domin ya bayyana a ranar da Allah Ya yi alkawari wanda kuma wannan daga cikin asirran Ubangiji babu wanda ya san su sai Allah. Ba zai gagara ba cewa wannan rayuwa tasa mai tsawo da dogon zamaninsa su zama Mu'ujiza da Allah Ta'ala Ya ba shi, kuma wannan ba ta fi Mu'ujizar kasancewarsa Imami yana dan shekara biyar kawai ba, yayin da mahaifinsa ya koma ga Ubangiji6 Madaukaki, kuma ba ta fi Mu'ujizar Annabi Isa (A.S.) girma ba yayin da ya yi magana da mutane yana cikin shimfidar jaririnsa yana yaro, kuma aka aike shi Annabi ga mutane. Tsawon rayuwa fiye da dabi'a kuwa, ko kuma ga wanda ya dauka cewa ta dabi'a ce - fannin Likitanci ba zai hana ta ba kuma ba zai shamakance ta ba, sai dai kawai cewa ilimin likita bai kai matsayin da zai iya kara tsawon rayuwar mutum ba, idan kuwa har ya gaza ai Allah Ta'ala mai iko ne a kan kome, kuma haka ya auku tabbatacce an tsawaita rayuwar Annabi Nuhu7 (A.S.) da wanzar da Annabi Isa8 (A.S.) kamar yadda Alkur'ani ya bayyana. Idan kuwa mai shakka ya yi shakku game da abinda Alkur'ani ya ba da labari game da shi to musulunci kam sai wata rana. Abin mamaki ne har Musulmi ya tsaya yana tambaye-tambaye game da yiwuwar haka alhali kuwa yana da'awar imani da Littafi Mabuwayi. Daga cikin abinda lalle ne mu ambata shi a nan shi ne cewa zamanin jiran ba wai yana nufin cewa musulmi su nade hannuwansu ba ne game da al'amuran da suke na gaskiya dangane da addininsu da abinda ya wajaba na taimaka masa, da jihadi a tafarkinsa, da riko da hunkunce-hukuncensa, da yin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna. Bilhasali ma musulmi dimin da'iman an kallafa masa ya yi aiki da abinda Allah Ya saukar na daga hukunce-hukuncen Shari'a kuma ya wajaba a kansa ya yi kokarin sanin su ta fuska ingantacciya, kuma wajibi ne a kansa ya yi umarni da kyakkyawa kuma ya yi hani da mummuna gwargwadon abinda ya iya kuma ikon yin haka ya samu gare shi:'Dukkanku makiyaya ne kuma dukkanku ababan tambaya ne game da abin kiwonsa."9 Don haka bai halatta gare shi ba ya jinkirta wajibansa don kawai yana jiran Mahadi (A.S.) mai kawo gyara, mai shiryarwa, wanda aka yi albishir da shi, domin wannan ba ya sauke aikin da aka kallafa, kuma ba ya jinkirta aiki, ba ya sa mutane su zama sun bar aiki.
1-Al- Gaibatu na Tusi shafi na 148 da 187, da Umdatu na Ibinil Batrik shafi aa 433 hadisi na 909 da shafi na 436, hadisi na 920, da Isbatul Hudat Juzu'i na 3 shafi na 504 hadisi na 303-304 da Sunan Abi Dawud Juzu'i na 4 shafi na 107 hadisi na 4284, da Sunan Ibin Majah Juzu'i na 2 shafi na 1368 hadisi na 4086 da dukkan hadisan Al- Babul 34 Kitabul Fitan, da Mustadrakul Hakim Juzu'i na 4 shafi na 557 Al- Mu'ujamul Kabir na Tabarani Juzu'i na 23 shafi 267 hadisi na 566, da Kifayatut Talib shafi na 486, da Kanzul Ummal Juzu'i na 14 shafi na 264 hadisi na 38662, Sunan Tirmizi Juzu'i na 4 shafi na 505, Al-Bayan fi Akhbari Sahibuz Zaman shafi na 479, Al- Hawi na Fatawi Juzu'i na 2 shafi, Al- Burhan Fi Alamatul Mahdi (A.S.) shafi na 94. 2- La'alla daga cikin masu rikitarwar Dokta Rundasan wanda yake cewa: "Lalle mai yiwuwa ne kwarai cewa rashin cin nasarar hukumar Ummayyawa na zahiri wajen kasa kafa rukunan adalci da daidaito a zamaninsu shekara ta 41-132 na daga cikin abubuwan da suka sabbaba akidar Mahadi a karshen zamani." Littafin Akidar Shi'a shafi na 231. 3- Kisaniyawa: Jama'a ce da suka yi ittifaki a kan Imamancin Muhammad Bin Hanafiyya. Wasunsu sun ce lalle Muhammad Bin Hanafiyya shi ne Imami bayan Mahaifinsa Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) domin Imam Ali (A.S.) ya ba shi tuta ranar Yakin Jamal inda ya ce da shi: Soke su suka irin na Mahaifinka a yabe ka, babu alheri a yaki matukar ba ka gwabza ba.
Wasunsu kuma sun ce: Lalle Imami bayan Imam Ali (A.S.) shi ne Imam Hasan (A.S.) sai Husain (A.S.) sa'an nan kuma sai shi ya zamanto Imami bayan Imam Husain (A.S.) ya fita daga Madina zuwa Makka kafin aukuwar al'amarin Karbala. Wasunsu suna da ra'ayin cewa shi Muhammad Bin Hanafiyya yana raye bai mutu ba kuma wai shi ne Mahadi da ake saurare, wannan su ne wadanda marubucin wannan littafin ya yi ishara game da su a nan. Wasunsu kuma sun tafi a kan cewa ya rasu kuma Imami bayansa shi ne Imam Aliyu Binul Husain Zainul Abidin (A.S.). Daga cikinsu kuma akwai masu cewa: Imamanci bayansa ya koma ga Abi Hashim Bin Muhammad Ibin Hanafiyya, sa'an nan kuma su kansu sun saba a kan Imamanci bayansa. Wasunsu suka ce ya koma ga Muhammad Bin Ali Bin Abdullah, wasunsu na cewa bayansa Imamanci ya koma ga Bayan Bin Sam'an suna kuma raya cewa ruhin Allah Ya kasance a jikin Hashim sa'an nan Ya fita Ya koma jikin shi Bayan. Watakila an sa musu suna Kisiniyawa ne saboda Mukhtar Bin Abi Ubaidus Sakafi ya kasance shugabansu kuma an kasance ana yi masa Lakabi da "Kisana" domin shugaban dogaransa shi ne (Abu Umrata) kuma sunansa kisana ne kuma ya zurfafa wajen shi Mukhtar din. Wannan kuwa a bisa asasin cewa akidar Shi'a Imamiyya ita ce mafi daidai a gurinsu kan cewa shi Mukhtar mutum ne Salihi mai akida sahihiya, kuma ya kasance yana kira ga Imamancin Imam Sajjad (A.S.) yabo gare shi kuwa ya zo a harshen Imam Sajjad (A.S.), da Imam Bakir (A.S.) da Imam Sadik (A.S.) kamar kuma yadda yabo gare shi da kuma rashin zargi a kansa ya zo daga Malaman Shi'a kuma babu wanda ya zarge masa illa kalilan daga cikinsu. Abin kuma da ake jifan sa da shi duk kazafi ne da makiya domin su bata shi domin shi ne ya yunkura don ramuwar gayya da daukar fansa ga Imam Husain (A.S.) ya kuma kashe wadanda suka kashe shi da zuriyar gidansa a Karbala. Malamar Shi'a Imamiyya da dama sun yi rubuce-rubuce game da rayuwar shi Mukhtar da ayyukansa. A duba Al-Milal wan Nihal Juzu'i na daya shafi na 131, Al- Farku bainal Firak shafi na 38 da Firakus Shi'a shafi na 23. 4- Domin tabbatar maganar Allah Ta'ala da ke cewa: "Shi ne wanda ya aiko Mazonsa da shiriya da addinin gaskiya don Ya tabbatar da shi a kan dukkan adddinai baki daya." Surar Tauba: 33, Fathi: 28, saf: 9. Domin ya zo a ruwayoyi da hadisai da dama daga Annabi (S.A.W.A) da kuma daga Imamai (A.S.) game da bayyanar Mahadi (A.S.) daga 'ya'yan Fatima (A.S.), kuma cewa zai cika kasa da daidaito da adalci bayan an cika ta da zalunci da rashin daidai kamar yadda ya riga ya gabata. Sidi Shahid Sadr ya ambata nassi kamar haka: "Akidar Mahadi a matsayinsa na shugaba da ake jira domin canja duniya zuwa ga mafi dacewa, hadisai da dama daga Annabi (S.A.W.A) baki daya da kuma daga Imamai (A.S.) a kebe, kuma sun yi ta'akidi a nassosi masu yawa ta yadda ba zai yiwu a yi shakku a kansu ba, an kidaya hadisai dari hudu daga Annabi (S.A.W.A) daga bangaren 'Yan'uwanmu Ahlus Sunna, kamar kuma yadda aka kididdige hadisai dangane da Imam Mahadi (A.S.) daga bangaren Shi'a da Sunna inda adadinsu ya kai sama da dubu shida. Wannan adadi ne mai yawan gaske wanda babu kamarsa a cikin sauran al'amuran musulunci bayyanannu, wadanda a bisa dabi'a musulmi ba ya shakka a kansu." Al- Bahas haulal Mahadi shafi na 63. 5- Saboda abinda ya gabata cewa kasa ba ta zama ta tsiraita daga hujja ba. 6- Ya zo a ruwayoyi cewa Imam Askari (A.S.) ya yi wafati a shekarar 260 a lokacin kuma shekarar Imam Mahadi (A.S.) shekara biyar kuma ya dauki nauyin Imamanci. Ruwayar Abil Adyan wanda ya kasance yana yi wa Imam Askari (A.s) hidima yayin da Imam din (A.S.) ya aike shi ya kai wasu littafa zuwa wasu birane lokacin da yake rashin lafiya, ya ce masa, lalle za ka boyu kwana goma sha biyar kuma ranar kwana na goma sha biyar din za ka shiga garin Samurra kaji ka kiyaye. Sai Abul Adyan ya tambaye shi game da Imamin bayansa sai ya ce masa shi ne wanda zai neme ka da amsoshina kuma ya yi mini salla kuma zai ba ka labarin abinda ke cikin buhun da ke tare da kai. Wannan kuwa duk abinda Imam ya fade haka ya auku. Abul Adyan ya dawo wanda ya nemi amsoshin shi ne Imam Mahadi (A.S.) kuma shi ne ya yi wa mahaifinsa salla bayan ya sallami baffansa sa'an nan kuma ya ba wa Abul Adyan labarin abinda ke cikin buhun da ke tare da shi, kamar kuma yadda ya bawa mutane da dama labarin wasu al'amura da babu wanda ya san da su sai su kansu, a wannan lokacin shekararsa biyar. A duba Kamaluddin wa Tamamun Ni'ima Juzu'i na 2 shafi na 476, da Biharul Anwar Juzu'i na 50 shafi na 332 hadisi na 4 da Tarikhu Ghaibatus Sugra shafi na 282 da abinda ya biyo baya. 7- Domin Yana cewa: "Kuma lalle hakika Mun aiki Nuhu ga mutanenSa ya kasance a cikinsu shekara dubu ba hamsin sai ambaliyar ruwa ta kama su alhali su suna azzalumai." Surar Ankabutu: 14. Kuma tabbatacce ne cewa wannan gwargwadon shekarun lokacin zamansa a cikin mutanensa ne kawai amma shekarunsa duka-duka an ce akalla dubu da dari shida ne an ce ma sun fi haka. Tafsirul Kasshaf Juzu'i na 3 shafi na 200 Tafsirul Ibin Kasir Juzu'i na 3 shafi na 418, da Zadul Masir na Ibinul Jauzi Juzu'i na 6 shafi na 261. 8- "Da fadarsu; Lalle ne mun kashe Al-Masihu Isa dan Maryama Mazon Allah", alhali kuwa ba su kashe shi ba, kuma ba su tsire shi ba sai dai an kamanta shi gare su ne. Lalle ne wadanda suka saba wa juna a kan sha'aninsa suna shakka game da shi, ba su da wani ilimi face bin zato, kuma basu kashe shi ba a hakika. Sai dai Allah ya dauke shi ne zuwa gare Shi. Kuma Allah Ya kasance Mabuwayi, Mai hikima" Surar Nisa'i: 157-158. 9- Jami'ul Ahadis na Kummi shafi na 21 da Jami'ul Akhbar Shafi na 337 hadisi na 919, Sahih Bukhari Juzu'i na 2 shafi na 6 da Juzu'i na 3 shafi na 196, Musnad Ahmad Juzu'i na 2 shafi na 5 Sunan Baihaki Juzu'i na 6 shafi na 287