Mun yi Imani cewa asalin Imamanci na daga
cikin jiga-jigan addini kuma imani ba ya cika sai da imani da shi kuma bai
halatta a kwaikwayi iyaye a kan haka ba, ko kuma zuriya ko masu tarbiyya kome
girmansu da darajarsu kuwa, sai dai ma ya wajaba ne a nemi sani a yi bincike a
game da shi kamar yadda ya wajaba a yi a kan Tauhidi da Annabci.
Alal
akalla imani da sauke nauyin da ke kan mukallafi yana daga cikin wajiban
shari'a wadanda aka wajabta masa kuma sun dogara ne a kan Imani da su
tabbatarwa ko korewa koda kuwa ba jigo ne daga cikin jiga-jigai da a kwaikwayi
wani a kansu ba saboda shi kansa ta wannan kwibin wajibi ne a yi imani da shi.
Wato ma'ana ta bangaren wajabcin sauke nauyin da ya wajaba a kansa tabbatacce
daga Allah Ta'ala da kuma a hankalce; kuma ba dukkansu ne aka san su ta fuskar
matabbacin dalili ba don haka babu makawa a koma ga wanda muka san cewa tabbas
bin sa zai kai mu ga sauke nauyin da ya wajaba a kanmu, wato mu koma ga Imam ga
wanda ya yi Imani da Imam ko kuma wani da ba Imam ba ga wadanda suka yi imani
da wanin Imam.
Kazalika mun yi imani cewa Imamanci
tausasawa ne daga Allah kamar Annabci. Don haka babu makawa a kowane zamani ya
zamanto , akwai Imami mai wakiltar Annabi a aikinsa na shiryar da bil Adama ,
da dora su a kan abinda yake maslaha a Sa'adar duniya da Lahira kuma biyayyar
da Annabi ya cancata daga mutane baki daya shi ma ya cancata domin tafi da
al'amuransu da maslaharsu, da tabbatar da adalci a tsakaninsu, da gusar da
zalunci da kiyayya daga tsakaninsu.
A
bisa wannan asasin Imamanci ya zamanto ci gaban aikin Annabci, dalilin kuma da
ke wajabta aiko da Annabawa da Manzanni ne ainihin wanda ke wajaba ayyana Imami
bayan Manzon Allah.
Wannan
kuma shi ne dalilin da ya sa muke cewa: Lalle Imamanci ba ya taba yiwuwa sai da
nassi daga Allah Ta'ala a bisa harshen Annabi ko kuma a bisa harshen Imamin da
ya gabata; kuma Imamanci ba nadin ko zabin kowa ba ne a tsakanin mutane, ba wai
al'amarinsu ba ne da idan suka so za su dasa wanda suke son dasawa ko kuma su
ayyana wanda suka son ayyanawa ya zama Imami a gare su, ko kuma a duk lokacin
da suka so barin ayyanawar sai su bari su zama haka nan sakaka ba su da Imami
bil hasali ma "Duk wanda ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba to ya mutu ne
mutuwa irin ta jahiliyya" kamar yadda haka ya tabbata daga Manzon Allah
(S.A.W.A.) a hadisi.
A
bisa wannan asasin ba zamani daga zamuna da zai zamanto babu Imami wanda aka
wajabta yi masa biyayya ba a cikinsa, wanda kuma Allah ne Ya nada shi, sawa'un
mutane sun ki ko ba su ki ba, sawa'un sun taimake shi ko sun ki taimakon sa,
sawa'un sun yi masa biyayya ko sun ki yi masa biyayya, sawa'un yana hallare ne
ko kuwa yana suturce ne daga idandunan mutane - domin kamar yadda ya inganta
Annabi (S.A.W.A.) ya suturtu daga ganin mutane, kamar yadda ya suturtu a cikin
kogo wanda game da shi Allah Ta'ala ke cewa: "Idan ma ba ku taimake shi ba
to ai Allah Ya riga Ya taimake shi yayin da wadanda suka kafirta suka fitar da
shi yana na biyun su biyu yayin da suke cikin kogo yayin da yake cewa
ma'abucinsa kada ka damu lalle Allah na tare da mu, sai Allah Ya saukar da
natsuwarSa gare shi Ya kuma taimake shi da rundunoni da ba ku gan su ba, kuma
Ya sanya kalmar wadanda suka kafirta makaskanciya kalmar Allah kuma ita ce
Madaukakiya kuma lalle Allah Mabuwayi ne Mai hikima" Surar Tauba: 40.
Ko
kuma kamar yadda ya suturtu a wadi, to haka nan ya inganta Imami ya suturtu
kuma babu bambanci tsakanin fakewa mai tsawo da gajera a hankalce.
Allah
Ta'ala Yana cewa: "Kuma ga kowace a'luma akwai mai shiryarwa." Surar Ra'ad: 7.
"Kuma babu wata al'umma face mai
gargadi ya zamanto cikinta." Surar Fatir: 24.
Imamanci shi ne jigo na hudu a
cikin jiga-jigan musulunci a gurin Mazhabar Ahlul Bait Masu bin Imamai goma sha
biyu, wato Shi'a Imamiyya, Imamanci kuma yana bayan Annabci a muhimmanci kuma
za'a iya cewa ita ce ka'idar da ke bambance Mazhabar Imamiyya daga sauran
Mazhobabi na Musulunci; kuma Imamanci asasi ne na tunani da Mazhabar mabiya
Ahlul Baiti suka gina Mazhabarsu a kai.
Imamanci: a lugga yana nufin shigewar gaban wani mutum domin sauran mutane su
bi shi su yi koyi da shi, don haka Imami shi ne wanda mutane suke koyi da shi,
mutanen da ke bin sa kuma su ne mamu. Jam'insa kuma shi ne Imamai. Kalmar Imami
ta zo a Alkur'ani har sau goma sha biyu gurare dabam-daban. Akwai guraren da ta
zo da sigar mufradi ba jam'i ba har sau bakwai a: Surar Bakara aya ta 124 da
Surar Hudu: 17 da Surar Hijri aya ta: 79 da Surar Isra'i aya ta: 71 da Surar
Furkan aya ta 74 da Surar Yasin aya ta 12, da Surar Ahkaf aya ta 12.
Sa'an nan kuma akwai guraren da ta zo da sigar jam'i sau biyar wadanda su ne
kamar haka: "Surar Taubati:12, Surar Anbiyai aya ta 73, Surar Kasas aya ta
5 da kuma ta 41 da Surar Sajdati aya ta 24".
Ma'anarsa ta Ka'ida kuwa Imamanci yana nufin: Mukami ne da Ubangiji Allah kan
zabi bayinSa ya ba su kamar yadda yake zaben Annabawa, kuma yakan umarci Annabi
ya sanar wa al'umma wannan Imamin ya kuma umarci mutane da su yi masa biyayya.
Mutane ba su da wani ikon su zaba wa kansu Imami: Allah Ta'ala yana cewa:
"Kuma Ubangijinka yakan yi halitta kuma Yana zabe su ba su da wani
zabi." Surar Kasas: 68.
Shi Imami ya bambanta da Annabi ne da cewa Annabi ana yi masa wahayi shi kuwa
Imami ba a yi masa wahayi, shi Imami yana karbar hukunce-hukunce ne daga Annabi
da shiryarwar Ubangiji. Don haka shi Annabi mai isar da sako ne daga Allah
Hadisai da dama da ke nuna cewa kasa ba ta taba zama babu Hujja. A duba Usul
Kafi Juzu' i na 1 shafi na 136 Babun Annal Aradha la Takhlu minal Hujja, da
kuma na 137 Babun Annahu Law Lam yabka fil Ardhi Illa Isnani La kana Ahaduhuma
Hujjira
shi kuma Imami mai isarwa ne daga Annabi.
Wannan shi ne abinda Mazhabar Ahlul Bait ke nufi da Imamanci.
Amma a gurin sauran Mazhabobi kuwa Imamanci na nufin shugabanci ne na gaba daya
a kan al'amuran addini da al'amuran duniya don Halifantar Annabi (S.A.W.A.) da
hukunce hukuncensa a rassan al'amuran ibada. Domin karin bayani a duba littafan
luga, da Aslus Shi'a wa Usuliha da Al'aka'iduj Ja'afariyya da Milal Wan Nihal
na Shahristani da Sharhil Makasid.
Allah Ta'ala Yana cewa: "Mu Mune
Muka aika Manzo mai albishir kuma mai gargadi kuma babu wata al'umma face mai
gargadi ya je mata". Surar Fatir: 24.
Ya riga ya shahara a tsakanin
malaman addinin Musulunci game da sanya Imami akwai maganganu biyu da ba su da
na uku. Akwai masu cewa Imamanci ra'ayi ne kuma zabin mutane ne ke ayyana shi.
Akwai kuma wadanda ke cewa ayyanawa ne daga Allah. Kuskuren ra'ayi na farko abu
ne da shi'a Imamiyya suka yi ittifaki a kai domin wajibi ne Imami ya zama Allah
ne Ya ayyana shi kuma shi kuma Annabi ya nuna shi ya kuma yi wasici da yi masa
biyayya bayansa - wato kamar yadda Manzon Allah (S.A.W.A.) ya yi a Ghadir Khum
- sa'annan shi kuma Imamin sai ya yi wasici da biyayya ga mai zuwa bayansa kuma
ya sanar da shi, haka nan za a yi ta yi bi da bi. Ko kuma a ga wata Mu'ujiza ta
bayyana a hannunsa domin "Isma" Sharadin Imamanci ce kuma tana daga
boyayyun al'amura wadda babu wanda ya san ta sai Allah Ta'ala.
Su kuwa sauran Mazhabobi da ba Imamiyya ba cewa suka yi:
Imamanci ba a shardanta nadawar Annabi ko alkawartawarsa game da shi ba, yana
iya zama ta hanyar yin Mubaya'a, wato shi ne malamai masana halal da haram su
yi wa wani mutum guda mubaya'a su sanya shi Imami - wannan kuwa yana ginuwa ne
a kan sharadin rashin "Isma" ga shi Imamin kuma ba sharadi ba ne ya
zamanto duka kowa da kowa ya yi masa mubaya'a hatta mubaya'ar mutum guda ma
tana iya wadatarwa. Idan kuwa har Mubaya'ar ba ta yiwu ba to akwai wata hanyar
nada Imamin: Tilastawa da kankanewa, idan Imami ya mutu wani wanda ya cika
sharuda ya maye gurbinsa ba tare da an sanya shi ko an yi masa mubaya'a ba ya
kuma tilastawa mutane kansa to halifancinsa ya tabbata koda kuwa fasiki ne
Jahili, Ja'iri, Azzalumi kuma suka ce bai halatta ba a tsige Imami koda kuwa
fasiki ne amma idan da wani da ya fi shi karfi zai zo ya kifar da shugabancinsa
ya kuma tilasta kansa a kan mutane to da shi ma ya zama Imami.
Tambaya a nan ita ce shin hankali yana yarje wa mutum ya bi mazhabar da ke
wajabta biyayya ga Imami fasiki, ja'iri, jahili ba don kome ba sai dan kawai
shi ne ya fi karfi da kudurar tilasta kansa a kan wasu koda ta hanyar fasikanci
da ja'irci?
Kuma bai halatta a cire shi ba sai dai da wanda ya fi shi karfi ya tilasta
shi sa'an shi ya zamanto shi ne Imamin? Shin wannan shi ne Imamin da idan mutum
ya mutu bai san shi ba ya mutu mutuwar jahiliyya? To wannan Mazhabar ina
matsayinta game da maganar Allah Ta'ala cewa: "Shin wanda yake shiryarwa
zuwa ga gaskiya shi ne ya fi cancantar a bi shi ko kuwa wanda ba ya shiryarwa
sai an shiryar da shi, me ya same ku kuke hukunta haka?" Surar Yunus: 35.
A duba Littafin "Nahjul Hakk wa kashussidki shafi na 168. Da sharhul
Makasid na Taftazani Juzu'i na 5 shafi na 233, da At- Tamhid na Bakilani: 168
da Aslus shi'a wa Usuliha 22'da Aka'idi Ja'afariyya: 29.
Al- Kafi Juzu'i na 1 shafi na 377
hadisi na 3 da Al- Mahasin Juzu'i na 1 shafi na 176 hadisi na 273, da Uyuni
Akhbarir Ridha (A.S.) Juzu'i na 2 shafi na 58 hadisi na 214 da Kamaluddin shafi
na 413 Hadisi na 15, da Al-Gaybatu na Nu'umani shafi na 130 hadisi na 6, da
Rijal Al- Kasshi Juzu'i na 2 shafi na 723 hadisi na 799, da Musnad Al- Tayalasi
shafi na 259 hadisi na 1913, da Hilliyatul Awliya'u Juzu'i na 3 shafi na 224 da
Al- Mu'ujamul Kabir na Tabarini Juzu'i na 10 shafi na 350 hadisi na 10687, da
Mustadrakul Hakim Juzu'i na 1/77 da Sharhun Nahjul Balaga na Ibin Abil Hadid
Juzu'i na 9 shafi na 155 da Yanabi'ul Muwadda Juzu'i na 3 shafi na 155 da
Majma'uz Zawa'id Juzu'i na 5 shafi na 224 da Musnad Ahmad Juzu'i na 4 shafi na
96.
Wadi shi ne fili tsakanin duwatsu
biyu. Wadin da ake nufi a nan shi ne wadin da ake kira "Wadin Abi Talib
(A.S.) wanda Bani Hashim da Banu Abdul Mutallibi bin Abdu Manaf, in banda Abu
Lahab, suka shiga cikinsa har na tsawo shekaru biyu ko kuma uku yayin da
Kuraishawa suka sanya masu fago don kada wani ma ya kai musu abinci. A duk
tsawan wannan lokacin sun kasance suna amfani da dukiyan Nana Khadija ne da ta
Abu Talib har suka kare. A lokacin ba su kasance suna fita daga wannan wadi ba
sai dai lokacin Umura a watan Rajab da kuma lokacin aikin Hajji. A wannan
lokacin Aliyu bin Abi Talib (A.S.) shi ne ya kasance yana fita a boye zuwa
Makka yana samo musu abinci.
A duba As- Sahih Fi Siratin Nabi Juzu'i na 2 shafi 108, da Lisanil Arab Juzu'i
na 1 shafi na 499.
Idan kun yi jayayy acikin wani abu ku mayar da shi ga Allah da Manzo
idan kun kasance masu imani da Allah da Ranar Lahira wannan shi ne aiheri kuma
mafi kyau." Surar Nisa'i: 59.
1- Ya zo daga Imam Bakir (A.S.) da kuma Imam Abi Abdullah Sadik (A.S.) cewa sun
ce: "Mu mu ne al'umma tsakatsaki, mu mu ne shaidun Allah a kan halittunSa". Al-Kafi Juzu'i na 1
shafi na 146 Hadisi na 2 da na 4 inda ayar nan ta zo "Haka nan muka sanya
ku al'umma matsakaiciya domin ku kasance shaidu a kan mutane Manzo kuma ya zama
shaida a kanku". Surar Bakara: 143.
2- Saboda su su ne Imamai na gaskiya, ya zo daga Manzon Allah (S.A.W.A.) ta
fuska maruwaita da dama cewa: "Duk wanda ya mutu bai san Imamin zamaninsa
ba to ya mutu mutuwar jahiliyya" A duba Abinda Muka Yi imani da shi game
da Imamai.
Ya zo daga Amirul Muminina Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) cewa: "Lalle idan da
Allah Ya so hakika da Ya sanar da bayinSa kansa amma Ya sanya mu kofofinSa, da
tafarkinSa, da hanyarSa, da kuma mafuskantarSa da ta nan ne ake zo maSa, duk
wadanda suka fandare da shugabancinmu ko kuma suka fifita wani a kanmu to lalle
su sun tabe daga kan tafarki." Al Kafi: 192.
3- Kazalika ya zo daga Imam (A.S.) cewa "Mu mu ne taskokin ilimin Allah,
kumu mu ne masu fassarar wahayin Allah, kuma mu mu ne hujjar Allah cikakkiya a
kan wadanda ke koma bayan sama, da wanda ke doron kasa." Al-Kafi: Juzu'i
na 1 shafi na 192.
Kazalika ya zo daga Imam Sadik (A.S.) cewa: "Mu mu ne Shugabanni a kan
al'amuran Allah, kuma taskar ilimin Allah kuma ma'ajiyar wahayin Allah"
Al- Kafi Juzu'i 1 shafi na 192.
4- A duba Sahifatul Imam- Ridha (A.S.) shafi na 47 hadisi na 67, da kuma Uyuni
Akhbarir Ridha (A.S.) Juzu'i na 2 shafi na 27 hadisi na 14, da Ilalis Sharai'i
Shafi na 123 Hadisi na 1 da Kamaluddin Juzu'i na 1 shafi na 205 hadisi na 19 da
Fadha'ilu Ahmad: Shafi na 189 Hadisi na 267 da Mu'ujamul Kabir na Tabarani
Juzu'i na 7 shafi na 25 Hadisi na 6260 , Matalibul Aliya Juzu'i na 4 shafi na
74 Hadisi na 4002, da Ihya'ul Mayyit Bi Fadha'ili Ahlul Bait na Suyuti, Shafi
na 42 hadisi na 21, da Zakha'irul Ukba shafi na 17, Fara'idus Sumtain Juzu' i
na 2 shafi na 241 hadisi na 515, da Kanzul Ummal Juzu'i na 12 shafi na 101
Hadisi na 34188, da Mustadrak na Hakim Juzu'i na 3 shafi na 149, da Majma'uz
Zawa'id Juzu'i na 9 hadisi na 174, da Sawa'ikul Muhrika shafi na 234.
5- Malaman tafsiri sun yi ittifaki kuma an ruwaito daga Imaman Ahlul Bait
(A.S.) da kuma sahabbai da dama cewa fadar Allah Ta'ala: "Abin sani kawai
shi ne cewa Allah Yana nufin kawai Ya tafiyar muku da datti ne Ya ku Mutanen
gida kuma Ya tsarkake ku sosai " Surar Ahzab: 33.
6- Cewa wannan ayar ta sauka ne game da Manzon Allah (S.A.W.A.) da Aliyu (A.S.)
da Fatima (A.S.) da Hasan (A.S.) da Husain (A.S.) kuma wannan shi ne abinda
marubucin littafin ya yi ishara da shi.
Domin karin bayani a duba: Nahjul Hakk shafi na 173, da Shawahidut Tanzil na
Haskani Juzu'i na 2 shafi na 10 Hadisi na 192, da Durrul Mansur Juzu'i na 5
shafi na 198, da Mushki Lil Asar Juzu'i na 1 shafi na 332, da Majma'uz Zawa'id
Juzu'i na 9
shafi na 121; da Musnad Ahmad Bin
Hanbal Juzu'i na 1 shafi na 330 da Juzu'i na 4 shafi na 107 da Juzu'i na 6
shafi na 292, da Sawa'ikul Muhrika shafi 85, da Tafsirut Tabari Juzu'i na 22
shafi na 5 da Usudul Ghabati Juzu'i na 4 shafi na 29, da Khasa'isun Nisa' i
Shafi na 4, da Al-Gadir Juzu'i na 1 shafi na 49 da Juzu'i na 3 shafi na 195 da
Juzu'i na 5 shafi na 416 da Ihkakul Hakk Juzu'i na 2 Shafi na 501-553 da kuma
Juzu'i na 5 shafi na 54, 55, 58 da kuma Juzu'i na 9/69-1 da Juzu'i na 18 shaf
na 359-383, da Dala'ius Sidki Juzu'i na 2 sahfi na 103, da Sahih Muslim Juzu'i
na 4 shafi na 1883, Sunan Tirmizi Juzu'i na 5 shafi na 351, da Tafsirin Ibin
Kathir Juzu'i na 3 shafi na 493.
7- Tunda yake Manzon Allah (S.A.W.A.) game da Aliyu bin Abi Talib (A.S.) a
hadisin Gadir "Ya Allah so wanda ya ka so shi, Ka ki wanda ya yi kiyayya
da shi Ka tozartu wanda ya tozarta shi Ka sanya gaskiya ta juya tare da shi duk
inda ya juya." Bayani game da haka zai zo a sashen bayanin Abinda muka yi
imani da shi cewa Imamanci da nassi ne.
8- Saboda cewa Imami sanarwa ce daga Manzon Allah (S.A.W.A.) kuma da yake
Manzon Allah (S.A.W.A.) ya fada da nassi cewa: "Duk wanda na kasance ni
shugabansa ne to ga Aliyu shi ma shugabansa ne." Wannan yana nufin cewa
da'a ga Imam da'a ce ga Manzo (S.A.W.A.) kuma yin watsi da hukuncinsa tamkar
watsi da hukuncin Manzo ne, Allah Ta'ala Ya ce: "Duk wanda ya bi Manzon
Allah to ya bi Allah ne." Surar Nisa'i: 80.
9- Ya zo daga Abi Hamza cewa daga Imam Sajjad (A.S.) cewa: "Aliyu Binul
Husain (A.S.) ya ce mana: Wane guri ne mafifici? Sai muka ce Allah da ManzonSa
da dan ManzonSa su ne suka fi sani, sai ya ce mana guri mafifici shi ne
tsakanin Makama Ibrahim (A.S.) da Rukun, kuma koda mutum zai yi tsawon rai irin
na Annabi Nuhu (A.S.) wato shekaru dubu ba hamsin - yana azumtar yininsu yana
kuma tsayuwar kiyamullailin dararensu a wannan gurin sa'an nan yaje ga Allah ba
ya da biyayya ga shugabancinmu to wannan ba zai amfana masa kome ba."
Man La Yahdhuruhu Fakih Juzu'i na 2 shafi na 159 hadisi na 17, da Ikabul A'amal
shafi na 243 hadisi na 2, da Amali na Tusi shafi na 132 Hadisi na 209 Wasa'ilus
Shi'a Juzu'i na 1 shafi na 122 hadisi 308 da baki dayan hadisan Babi na 29 da
Babobin mukaddamar Al-Ibadat a Wasa'il Juzu'i na 1.
Al- Hakimul Haskani ya kawo hadisin da ke biye a littafin Shawahidut Tanzil
Juzu'i na 2 shafi na 141 daga Abi Amamal Bahili cewa: "Manzon Allah
(S.A.W.A.) ya ce: Allah Ya halitta Annabawa daga bishiyoyi dabam-daban, ni da
Aliyu kuma an halitta mu daga bishiya guda, ni ni ne tushenta Aliyu kuma
reshenta Hasan da Husain kuwa 'ya'yanta, Shi'awanmu kuma ganyayenta duk wanda
ya makale wa wani reshe daga rassanta ya tsira wanda kuwa ya kauce to ya
halaka, kuma idan da Bawan Allah zai yi bauta a tsakanin Safa da Marwa shekaru
dubu har ya zamanto kamar tsohon kirgi da fatarsa ta tattara amma bai samu
soyayyarmu ba Allah zai kifa shi a kan fuskarsa ranar Alkiyama, Sa'an nan sai
Manzo (S.A.W.A.) ya karanta wannan aya "ka ce ni ba na rokon ku wani lada
kansa sai dai soyayyar dangi makusata". Surar Shura: 23.
10- Sunan Tirmizi Juzu'i na 5 shafi na 663 Hadisi na 3788 da Musnad Ahmad
Juzu'i 3 shafi na 14 da 17 da 26, Juzu'i na 5 shafi na 182 da shafi na 189, da
Sunanud Darimi Juzu'i na 2 shafi na 431 da Al- Musannif na Ibin Abi Shaiba
Juzu'i na 11 shafi na 452 hadisi na 11725, da Sunan Ibin Abil Asim Juzu'i na 2
shafi na 336 hadisi na 754, da 628,m 630, 1548, 1549, 1553, 1555, da Tabakat na
Ibin Sa'ad Juzu'i na 2 shafi na 194 da Mushkilul Asar Juzu'i na 4 shafi na 368,
da Mustadrikul Hakim Juzu'i na 3 shafi na 109 da 148 da Hillayatul Awliya'i
Juzu'i na 1 shafi na 355 da Mu'ujamul Kabir na Tabarani Juzu'i na 5 shafi na
153-154 hadisi na 4921-4923 da hadisi na 169-170, 4980-4982, Mu'ujamul Sagir
Juzu'i na 1 shafi 131, da Al-Munakib na Ibin Magazili 234-235 hadisi 281-283,
da Masabihus Sunna Juzu'i na 4 shafi na 190 hadisi na 4816 da Jami'ul
Usul-Juzu'i na 1 shafi na 278 da Usudul Gaba Juzu'i na 2 shafi na 12 da
Zakha'irul shafi na 16 da Ihya'il Mayyit bi Fadha'ili Ahlit Baiti (A.S.) na
Suyuti shafi na 30-32 hadisi na 6-8 da Majma'uz Zawa'id Juzu'i na 1 shafi na
170 da kuma Juzu'i na 9 shafi 162, da Kanzul Ummal Juzu'i na 1 shafi na 172-173
hadisi na 870-873 da 875, 876, da 185-186 hadisi na 952-9S3 da Sahih Muslim
Juzu'i na 4 shafi na 1873 hadisi na 36 da 37, Tafsirur Razi Juzu'i na 8 shafi
na l63 da Tafsirin Ibin Kasir Juzu'i na 4 shafi na 122.
Bin
diddigin duKkan abinda ya zo na daga ruwayoyi da ayoyin Alkur'ani ba ya goyon
bayan cewa wannan sakon kagagge ne kazalika bayani manufofinsu da suke nuni da
su.6
Sa'an nan shi kuma kansa (A.S.) ya ba da
nassi game da Imamancin Hasan da Husain (A.S.), shi kuma Husain7 ya
ba da nassin Imamancin dansa Aliyu Zainul Abidin (A.S.) haka nan dai Imami ke
ba da nassin Imami bayan Imami, wanda ya gabata ya ba da na mai zuwa har zuwa
kan na karshensu kuma shi ne zababbensu kamar yadda zai zo.
1- ya riga ya gabata cewa Imami tamkar Annabi ne sai dai cewa Annabi ana yi
masa wahayi Imami
kuwa ba a yi masa wahayi.
2- Al- Musannaf na Ibin Abi Shaiba Juzu'i na 12 shafi na 67 hadisi na 1214
da 68 hadisi na 12141, da Sunan Ibin Majah Juzu'i na 1 shafi na 43 hadisi na
116, Sunan Tirmizi Juzu'i na 5 shafi na 633 hadisi 3713, da As- Sunna na Ibin
Abi Asim shafi na 59l hadisi na 1361, Musnad Ahmad Juzu'i na 118- 119 da kuma
Juzu'i na 4 shafi 281 da 368 da 370 da 372, da Khasa'is na Nisa'i shafi na 102
hadisi na 88, Ansabul Ashraf na Balaziri Juzu'i na 2 shafi na 156 hadisi na
169, da Kashful Astar na Bazari Juzu'i na 3 shafi na 190-191, da Al- Mu'ujamul
Kabir na Tabarani Juzu'i na 3 shafi na 21 hadisi na 3052 da kuma Juzu'i na 4
shafi na 173 hadisi na 4053, da Mu'ujamus Sagir Juzu'i na 1 shafi na 1 da shafi
na 65 da Mustadrakul Hakim Juzu'i 3 shafi na 109 da Akhbaru Isfahan Juzu'i na 1
shafi na 107 da Juzu'i na 2 shafi na 228 da Tarikhu Bagdad Juzu'i na 7 shafi na
377 da Juzu'i na 14 shafi 236, da Al-Manakib na lbin Magazili shafi na 16-27
hadisi na 23, 26, 27, 29, 33, 37, 38, da Shawahidut Tanzil na Haskani Juzu'i na
1 shafi na 157 hadisi na 211, da Tarikhu Dimashk na Ibin Asakir - Tarjamatul
Imam Ali (A.S.) Juzu'i na 2 shafi na 38-84 Tazkiratul Khawas shafi na 36, da
Usdul Ghaba Juzu'i na 1 : 367 da Juzu'i na 4 shafi na 28 da Zakha'irul Akba
shafi na 67, da AI- Isaba Juzu'i na I shafi na 304, don karin bayani kuma ana
iya duba Littafan- Al- Gadir na Shaikh Amini da littafin Ihkakul Hak, da
Abkatul Anwar da Dala'ilus Sidki da sauransu da dama.
3-Amali Saduk shafi na 523, A'alamul Wara shafi na 167, da Ihakak Hak Juzu'i na
4 shafi na 297, Musnad Ahmad Juzu'i na 111 da shafi na 159 , Khasais na Nisa'i
shafi na 83 hadisi na 66, da Tarikhut Tabari Juzu'i 19 shafi na 74, da
Shawahidut Tanzil Juzu'i na 1 shafi na 420 da Sharhin Nahjul Balaga na Ibin
Abil Hadid Juzu'i na 3 shafi 267, da Yanabi'ul Muwadda Juzu'i na 1 shafi na
104, Al- Kamil Juzu'i na 2 shafi na 62 da Majma'uz Zawa'id Juzu'i na 8 shafi
302 da sauransu, da ba za su kidayu ba.
4- Al- Musannif na Ibin Abi Shaiba Juzu'i na 12 shafi na 60 hadisi na 12125
da shafi na 61 hadisi na 12126, da Tarikhul Kabir na Bukhari Juzu'i na 1 shafi
na 115 hadisi na 333 da Juzu'i na 7 shafi na 301 hadisi na 1284, da Sahih
Muslim Juzu'i na 4 shafi na 1870 hadisi na 2404, da Sunanut Tirmizi Juzu'i na 5
shafi na 640 hadisi na 3730, Sunan na Ibin Abi Asim: Ya ambata shi da isnadai
dabam-daban daga hadisi na 1333-1348, Musnad Ahmad Juzu'i na 1 shafi na 179 da
Juzu'i na 3 shafi na 32, da Juzu'i na 6 shafi na 438, Khasa'is na Nisa'i shafi
na 68-79 hadisi na 45, 48, 50, 51, 62, 63, 64 da Hilliyatul Awli'ya'u Juzu'i na
4 shafi na 345 da Juzu'i na 7 shafi na 195 da 196 da Tarikhu Isfahan Juzu'i na
biyu shafi na 281, 328 da Mu'ujamul Kabir na Tabarani Juzu'i na 1 shafi na 146
hadisi na 328 da 148, 333, 334, da Juzu'i na 2 shafi na 247 hadisi na 2035, da
Juzu'i na 4 shafi na 17 hadisi na 3515 da Juzu'i na 11 shafi na 74 hadisi na
11087 da Juzu'i na 24 shafi na 146 hadisi na 384-389, da Mu'ujamus Sagir Juzu'i
na 2 shafi na 53,54, Tarikhu Bagdad Juzu'i na 1 shafi na 325 da Juzu'i na 3
shafi na 406, Juzu'i na 8 shafi na 53 da Juzu'i na 9 shafi na 365 da na 10
shafi 43, da'Juzu'i na 12 shafi na 323, da Isti'ab Juzu'i na 3 shafi na 34, da
Al-Manakib na Ibin Magazili shafi na 27-36 hadisi na 40-56, Tarikhu Dimashk
Tarjamatu Imam Ali (A.S.) Juzu'i na 1 shafi na 306-390, Majma'uz Zawa'id Juzu'i
na 9 shafi na 109 da sauransu.
5- Tafsiru Furatul Kufi shafi na 40-41, da Amalis Saduk shafi na 107 hadisi na
4, da Tafsirut Tibyan na Tusi Juzu'i na 3 shafi na 559, da Ihtijaj na Tabrisi
Juzu'i na 2 sha 489, da Tafsiriut Tabari Juzu'i na 6 shafi na 186, da Asbabun
Nuzul na Wahidi shafi na 113 da Al- Munakib na Ibin Magazili shafi na 3 12
hadisi na 356 da shafi na 313 hadisi na 357, Al-Manakib na Khawarzimi shafi
264, Tazkiratul Khawas shafi na 24, Tafsiri
|
Adadi |
Al-Kunya |
Suna |
Lakabi |
Haihuwa |
Rasuwa |
|
1 |
Abul Hasan |
Aliyu bn Abi Talib |
Al-Murtadha |
Shekara ta 23 Hijiriyya |
Shekara ta 40 Hijiriyya |
|
2 |
Abu Muhammad |
Al-Hasan bn Ali |
Az-Zakiy |
Shekara ta 2 Hijiriyya |
Shekara ta 50 Hijiriyya |
|
3 |
Abu Abdullah |
Husain bn Ali |
Sayyidush-Shuhada'u |
Shekara ta 3 Hijiriyya |
Shekara ta 61 Hijiriyya |
|
4 |
Abu Muhammad |
Ali bn Husain |
Zainul Abidin |
Shekara ta 38 Hijiriyya |
Shekara ta 95 Hijiriyya |
|
5 |
Abu Ja'afar |
Muhammad bn Ali |
Al-Bakir |
Shekara ta 57 Hijiriyya |
Shekara ta 114 Hijiriyya |
|
6 |
Abu Abdullah |
Ja'afar bn Muhammad |
Al-Sadik |
Shekara ta 83 Hijiriyya |
Shekara ta 148 Hijiriyya |
|
7 |
Abu Ibrahim |
Musa bn Ja'afar |
Al-Kazim |
Shekara ta 128 Hijiriyya |
Shekara ta 183 Hijiriyya |
|
8 |
Abul Hasan |
Aliyu bn Musa |
Ar-Ridha |
Shekara ta 148 Hijiriyya |
Shekara ta 203 Hijiriyya |
|
9 |
Abu Ja'afar |
Muhammad bn Ali |
Al-Jawad |
Shekara ta 195 Hijiriyya |
Shekara ta 220 Hijiriyya |
|
10 |
Abul Hasan |
Aliyu bn Muhammad |
Al-Hadi |
Shekara ta 212 Hijiriyya |
Shekara ta 254 Hijiriyya |
|
11 |
Abu Muhammad |
Al-Hasan bn Ali |
Al-Askari |
Shekara ta 232 Hijiriyya |
Shekara ta 269 Hijiriyya |
|
12 |
Abul Kasim |
Muhammad bn Hasan |
Al-Mahdi |
Shekara ta 256 Hijiriyya |
......... |