Annabta
Mun yi imani cewa Annabci aiki ne na Allah
Ta'ala, wakilci ne na Ubangiji, wanda shi Allah Ta'ala Yake daukar wadanda Ya
zaba daga cikin bayinSa salihai da waliyanSa kamilai a `yan Adamtakarsu, Ya
aika su zuwa ga sauran mutane domin shiryar da su ga abinda yake da amfani da
maslaha gare su a duniya da kuma lahira. Tare kuma da nufin tsabtace su da
tsarkake su daga daudar miyagun dabi'u da munanan al'adu kuma da koya musu
hikima da ilimi da bayyana musu hanyoyin Sa'ada da alheri domin `yan Adamtaka
ta kai ga kamalarta da ta dace da ita domin ta daukaka ga daraja madaukakiya a
gidajen duniya da na lahira
Kuma mun yi imani cewai Lalle ka'idar
tausasawa -wanda da sannu za mu yi bayanin ma'anarta nan gaba- ta sanya ya zama
babu makawa Allah Ya aiko ManzanninSa domin su shiryar da dan Adam, da kuma
isar da sokan gyara domin su zamanto wakilan Allah kuma halifofinSa.
Kamar
kuma yadda muka yi imani da cewa Allah Ta'ala bai dora wa mutane hakkin ayyana
Annabi ba ko kuma kaddamar da shi ko zaben sa. Ba su da wani zabe a kan haka, sai dai al'amarin haka ga Allah yake domin
"Shi ne Ya fi sanin inda zai sa sakonSa." Surar An'am ayata 124. Kuma
ba su da wani hukunci a kan wanda Allah zai aiko shi a matsayin mai shiryarwa,
mai albishir ko mai gargadi, kamar kuma
yadda ba su da wani hukunci a kan abinda ya zo da shi na daga hakunce-hukunce
da sunnoni da shari'a.
Imam Aliyu Bin Abi Talib (a.s.)
yayin da yake bayani ya siffanta fara halitta sama da kasa da halitta Annabi
Adam (A.S.) da kuma ambata Annabawa da aiko su ya fada a hudubarsa cewa:
"Kuma Subhanu Ya zabi Annabawa daga cikin `ya'yansa (Adam) Ya karbi
alkawarinsu a kan wahayi da kuma amanarsu a kan isar da sako. Yayin da yawancin
halittunSa suka canja suka jahilci hakkinSa, suka riki ababan bauta tare da Shi
shedanu suka fitsare su daga saninSa, suka yanke su daga bautarSa. Sai Ya aiko
musu da ManzanninSa, kuma Ya bibiyar musu da AnnabawanSa domin su sake shiryar
su ga alkawarin halittarsu, su tunatar da su mantattun ni'imominSa kuma su kafa
musu hujja da isar da sako, su farfado da abubuwan da hankali ya mance, su nuna
musu ayoyin kudura, na daga rufin da ke dage a samansu, da shinfidar da ke
sanye a karkashinsu da abincin rayuwarsu, da ajalin da ke kare su, da gajiya da
ke tsofar da su, da faruwar al'amura dake bibiye da su, kuma Allah bai taba
barin bayinSa babu Annabi aikakke ko kuma littafi saukakke ba, ko kuma wata
hanya bayyananniya ba. Manzanni da karancin mabiya ba ya sa su gaza ko kuma
yawan masu karyatawa gare su, duk wanda ya gabata daga cikinsu kan sanar musu
wanda zai zo daga bayansa ko kuma wanda ya zo daga baya ya sanar da wanda ya
gabance shi. A kan haka karnoni suka yi ta shudewa, zamunna suka yi ta wucewa,
iyaye suka yi ta gabata Annabawa suka yi ta biyowa, har Allah subhanahu ya aiko
Muhammadu Rasulullahi, sallallahu Alaihi wa alihi, domin aiwatar da alkawarinSa
da cika AnnabcinSa da Ya karbi alkawari a gurin AnnabawanSa wanda sunansa mashahuri
ne, haihuwarsa kuma mai girma ce. A lokacin mutanen bayan kasa al'ummu ne a
rarrabe, masu ra'ayoyin zukata dabam-dabam, da hanyoyi mabambanta, tsakanin
masu kamanta Allah da halittunSa, ko kuma wuce iyaka a sunanSa, ko kuma mai
nuni zuwa ga waninSa, sai Allah Ya shirye su da shi daga bata, ya tserar da su
da kokarinsa daga jahilci." Nahjul Balagha Huduba ta. 1.
Annabci Tausayawane
Lalle shi mutum halitta ne mai haddodi
masu ban al'ajabi, mai sarkafaffun gabobi a halittarsa da dabi'arsa da ruhinsa
da kuma hankalinsa, kai hatta ma a kan kowane daya daga cikin jama'arsa nauo'in
zaburar fasadi sun tattara a cikinsa kamar kuma yadda masu zaburarwa zuwa ga
alheri da gyara suka tattara a cikinsa ta bangare gudan.
Allah Ta'ala yana cewa: "Da rayi da
abinda Ya daidaita da kuma Ya cusa mata fajircinta da kuma takawarta."
(Surar Shamsi: 7-8) "Lalle shi mutum tabbatacce yana c ikin hasara."
Surar Asri: 2, da kuma "Lalle ne shi mutum tabbas yana dagawa. Don kawai
ganin ya wadata" Surar Alak: 6-7 "Lalle zuciya tabbas mai umarni da
mummuna ce". Surar Yusuf: 53. Da sauran ayoyi makamantan wadannan da ke
bayyanawa a sarari suna nuni ga irin yadda ran mutum ke kunshe da rauni da kuma
sha'awa.
A
bangare na biyu kuma, Allah Ta'ala Ya halitta masa hankali mai shiryarwa tare
da shi wanda zai kai shi zuwa ga gyara da kuma guraren alheri da kuma zuciya
mai gargadi da ke masa fada kada Ya aikata mummuna da zalunci tare da aibata
shi a kan aikata abinda yake
mummuna abin zargi.
Abokin husumar rai da ke cikin zuciya da
imani yana tsakanin aron raunanawa ne da kuma hankali. Duk wanda hankalinsa ya
yi galaba a kan rauninsa to yana daga cikin mafi kololuwar matsayi masu
shiryarwa a `yan adamtakarsu, kammalallau a ruhinsu wanda kuwa rauninsa ya
rinjaye shi to lalle yana daga cikin masu hasarar matsayi, masu taraddudi a yan
Adamtaka, masu faduwa zuwa matsayin dabbobi.
Mafi tsanani daga cikin wadannan masu
husuma biyu itace tausasawar zuciya da rundunarta. Don haka ne kake ganin
yawancin mutane sun dulmuye a cikin bata, suna nesa da shiriya ta hanyar bin
sha'awace-sha'awace da amsa kiran raunin zuciya, "kuma mafi yawan mutane
ba za su zama muminai ba koda kuwa ka yi kwadayin haka." Surar Yusuf 103.
Shi mutum saboda gazawarsa da rashin
saninsa game da abubuwan da ke kewaye da shi, da kuma rashin sanin asirran
abubuwan da ke kewaye da shi da ma wadanda ke bullowa daga cikinsa shi kansa,
ba zai iya sanin dukan abinda zai cutar da shi ko ya amfane shi ba shi da
kansa, ba kuma zai iya sanin abinda zai kai shi ga samun sa'ada ko ya kai shi
ga tsiyacewa ba, sawa'un a kan abinda ya kebatu da shi ne shi kadai ko kuwa
wanda ya shafi dan Adam baki daya da kuma al'ummar da ke kewaye da shi. Shi bai
gushe yana jahili kuma yana kara jahilci ne ko kuma kara fahintar jahilcinsa ne
duk yayin da iliminsa game da dabi'a ko kuma ababan halitta ya kara karuwa.
Saboda haka mutum a tsananin bukatarsa ta son kaiwa ga darajar sa'ada yana
bukatar wanda zai dora shi a kan hanya mikakkiya shararriya zuwa ga shiriya
domin rundunar hankali ta kara karfafa da haka har ya zamanto mutum zai iya yin
galaba a kan abokin gabarsa yayin da ya shiga fagen faman gwabzawa tsakanin
rundunar hankali da raunin tausasawar zuciya.
Yawanci
bukatar wanda zai kama hannunsa zuwa ga alheri da gyara na kara tsananta ne
yayin da tausasawar zuciya ke yaudarar sa ta hanyar nuna masa abinda yake
mummuna cewa mai kyau ne ko kuma kyakkyawa cewa mummuna ne ta nuna masa kyawun
fandarewarsa, ta rikitar masa hanyar gyara da sa'ada da ni'ima a lokacin da shi
ba shi da masaniyar da zai bambance dukan abinda yake mai kyau mai amfani da
kuma wanda yake mummuna marar amfani ga mai gaggawar kutsawa cikin wannan
arangamar ne ta yadda ya sani ko kuma ta inda bai sani ba sai dai wadanda Allah
Ya kubutar.
Saboda
haka abu ne mawuyaci ga mutum masanin ilimin zamani ya kai kansa ga dukan
tafarkunan alheri da amfani da kuma sanin dukan abinda zai amfane shi ko ya
cutar da shi a duniya da lahira ballantana kuma jahili; sawa'un al'amari ne da
ya kebe shi shi kansa ko kuma ya hada da al'umma da yake zaune a cikinta ne. Ba
ya taba kaiwa ga wannan masaniyar koda kuwa ya hada kai ya yi taimakekeniya da
sauran mutane da ke tare da shi ko da kuwa sun hadu sun yi bincike, koda kuwa
sunyi tarurruka da zama dabam-dabam da kuma shawarwari.
Don haka ne ya zama wajibi Allah Ta'ala Ya
aiko da Annabawa da manzanni a cikin mutane domin rahama da tausasawa gare su.
"Manzo daga cikinsu yana karanta musu ayoyinSa yana tsarkake su kuma yana
koya musu littafi da hikima" (Surar Juma'a: 2). Yana musu gargadi game da
abinda ke da cutarwa gare su kuma yana musu albishir game da abinda yake da
alheri da gyaruwa da sa'ada a gare su. Tausasawar daga Allah wajibi ne domin
tausasawa ga bayinSa na daga cikin tsantsan kamalarSa. Shi mai tausasawa ne ga
bayinSa, Mai yawan baiwa, Mai karimci, idan kuwa har ya zamanto a wani guri da
ya dace akwai bukatar Ya kwarara kyautarSa da tausasawa to babu makawa Ya zuba
tausasawarSa domin babu rowa a farfajiyar rahamarSa, babu nakasa da tawaya a
kyautarSa da karimcinSa.
Ma'anar
wajibi a nan ba wai tana nufin cewa wani zai umarce shi da aikata haka ba ne
har Ya zama tilas a kansa Ya yi wa wanda Ya yi umarni biyayya! Allah Ya daukaka
ga haka, ma'anar wajibi a nan tamkar ma'anar fadin da ake yi ne cewa shi Allah
wajibin samamme ne wato ba zai taba koruwa ba ba zai taba yiwuwa a raba shi da
samuwa ba.
Mu'ujizar Annabawa
Mun yi imani da ccwa lalle Allah Ta'ala tunda Yake sanya wa bayinsa mai shiryarwa
da kuma Manzo to babu makawa Ya sanar da shi gare su, Ya kuma nuna musu ko wane
ne shi a ayyane. Wannan kuwa ya
takaita ne a kan sanya musu wani dalili da kuma kafa musu hujja a sakon domin
cika tausasasarSa da kuma kammala rahamarSa.
Allah Ta'ala Yana cewa: "Manzanni
masu bushara da kuma gargadi domin kada mutane su zama suna da wata hujja a
gurin Allah bayan Manzanni kuma Allah Mabuwayi ne Mai hikima." Surar
Nisa'i: 165.
Wannan, kafa hujjar kuwa babu makawa ya
ramanto irin wanda ba ya samuwa sai daga mahaliccin halittu, mai sarrafa
samammu- wato ya zamanto abin ya dara kudurar dan Adam. Ya sanya shi a hannun
shi manzon mai shiryarwa, domin ya zamanto an san shi da shi kuma ya zamanto
mai shiryarwa zuwa gare shi wannan dalili da hujja shi ake kira mu'ujiza; wato
gagara badau saboda kasancewarsa ya gagari dan Adam, ya yi gasa da shi ko kuma
ya kawa makamancinsa.
Kamar
yadda babu makawa ga Annabi ya zo da mu'ujiza ya bayyana ta ga mutane domin ya
kafa musu hujja haka nan babu makawa wannan mu'ujizar ya nuna ta kuma yadda za
ta gagari malamai da kuma kwararrun zamaninsa; ballantana kuma sauran mutane,
tare kuma da danganta wannan mu'ujizar da ikrarin Annabci daga mai mu'ujizar,
saboda kasancewarsa yana da sadarwa ruhi da wanda yake jujjuya halittu.
Idan
wannan ya tabbata ga mutum, bayyanar mu'ujiza wadda ta saba wa al'ada, ya kuma
yi da'awar Annabci da sako, to a lokacin sai ya zamanto abin gaskatawar mutane
a kiran da yake yi, tare da yin imani da sakon nasa, da bin maganarsa da
umarninsa, sai wanda zai gaskata shi Ya yi imani da shi wanda zai ki kuma ya
kafirce masa.
Wannan shi ne abinda ya sa muka ga cewa
mu'ujizar kowane Annabi ta dace da ilimi da kuma fasahar zamaninsa. Mu'ujizar
Annabi Musa ita ce sanda wanda ke hadiye sihiri da abinda suke yin ba duhunsa
saboda kasancewar sihiri a zamaninsa shi ne fannin fasaha da yake mashahuri
yayin da sandan ya zo sai dukan abinda suke aikatawa ya baci suka san cewa
lalle wannan abu ne da ya fi karfinsu kuma ya dara irin fannin fasaharsu, lalle
wannan yana daga cikin abubuwan da, dan Adam ya gaza ya kawo shi kuma kwarewa
da ilimi sun dushe a gabansa. Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma sai muka yi
wahayi ga Musa kan cewa jefa sandanka sai ga shi yana hadiddiye abubuwan da
suke kirkirawa. Kuma gaskiya ta tabbata abinda suke aikatawa kuma ya baci. Sai
aka rinjaye a nan ,sa'annan suka koma suna kaskantattu. Kuma aka kifarda masu
sihirin suna sujada." Surar A'araf: 117-120.
Hakanan mu'ujizar Annabi Isa (A.S.) ita ce
warkar da makafi da masu albaras da kuma raya matattu saboda shi ya zo ne a
lokacin da likitanci shi ne fannin fasahar kwarewar da ke tsakanin mutane kuma
akwai malamai akwai likitoci da suke su ne manyan bokaye gare su sai iliminsu
ya gaza jeruwa da abinda Annabi Isa (A.S.) Ya zo da shi. Allah Ta'ala Yana
cewa: "Kuma Manzo zuwa ga Bani Isra'ila cewa lalle ni na zo muku da aya
daga Ubangijinku ni ina halitta muku daga laka abinda yake kamar surar tsuntsu
kuma in hura a cikinsa ya zamanto tsuntsu da izinin Allah kuma ina warkar da
makaho da mai albaras kuma ina raya mamata da izinin Allah kuma ina ba ku
labarin abinda kuke ci da wanda kuke taskancewa a gidajenku lalle a cikin
wannan akwai aya gare ku idan kun kasance muminai." Surar Al- Imran: 49.
Mu'ujizar Annabinmu madawwamiya ita ce
Alkur'ani saboda shi ya zo ne a lokacin ma'abuta ilimin balaga su ne kan gaba a
tsakanin mutane inda ya kure su da balagarsa da bayaninsa. Duk da fasaharsu da
balagarsu sai da Alkur'ani ya kaskantar da su ya rikitar da su ya fahintar da
su cewa su ba za su iya fito na fito da shi ba don haka suka sallama masa
rinjayayyu bayan sun gaza kasawa da shi, suka ma gaza isa ga kurar da ya tile
su da ita ya wuce ya barsu.
Allah
Ta'ala yana cewa: "Kuma idan da mutane da Aljannu za su taru a kan
su zoda kwatankwacin wannan Alkur'anin to da ba za su zo da makamancinsa ba
koda kuwa sashensu na taimakon sashe." Surar Isra'i: 88.
Kalubalantar su da ya yi kan cewa su kawo
sura goma suka kasa na tabbbatar da cewa lalle ya gagare su. Allah Ta'ala Yana
cewa: "Ko suna cewa shi ne ya kage shi ne ka ce to ku zo da surori goma
makamantansa kagaggu kuma ku kira duk wanda za ku iya wanda ba Allah in kun
kasance masu gaskiya" Surar Hud: 13
Sa'an nan kuma ya sake kalubalantar su kan
su kawo sura guda kamar sa suka gaza. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma idan
har kun kasance a cikin kokwanto daga abinda muka saukar to ku zo da sura guda
kamar sa kuma ku kira shaidunku da ba Allah ba in kun kasance masu
gaskiya". Surar Bakara: 23
Allah Ta'ala Yana cewa: "Ko suna cewa
ya kage shi ne ka ce ku zo da sura guda kamarsa kuma ku kira duk wanda za ku
iya ba Allah in kun kasance masu gaskiya". Surar Yunus: 38.
Ya sanar da mu yadda suka koma fito na
fito da hakora ba da harshe ba Ya sanar da mu cewa shi Alkur' ani wani nau'i ne
na mu'ujiza kuma Annabi Muhammad bin Abdullah ya zo da shi ne da kira da kuma
da'awar sako. Don haka muka san cewa Manzon Allah (S.A.W.A.) ya zo da gaskiya
da hakika kuma shi ma ya gaskata da shi, tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi.
Ismar Annabawa
Kuma mun yi imani da cewa Annabawa
ma'asumai ne, ba sa aikata sabo dukkaninsu kazalika Imamai kyakkyawar gaisuwa
ta tabbata a gare su. Mun saba da wasu daga cikin musulmi a kan haka don su ba
su wajabta isma (rashin aikata sabo) ga Annabawaballantana ma Imamai.
Isma:
Ita ce tsarkaka daga aikata zunubi da sabo kananansu da manyansu; da kuma
tsarkaka daga mantuwa , koda kuwa hankali bai kore aukuwar haka daga Annabi ba.
Sai dai kawai wajibi ne ya zamanto ya tsarkaka hatta daga dukkan abinda ke
zubar da mutunci kamar cin abu a kwararo a tsakanin mutane ko kuma kyalkyala
dariya da dai dukkan abinda bai dace a aikata shi ba a tsakanin mutane ba.
Dalilin
da ya sa Isma ta zama wajibi kuwa shi ne idan da har ya halatta Annabi ya
aikata sabo ko kuma ya yi kuskure, ko kuma wani abu makamancin wannan ya auku
daga gare su to kuwa lalle da biyayya gare su a aikin da suka aikata da sabo ko
kuskure bai wajaba ba, ko kuma da idan har ya wajaba to da mun halatta aikata
sabo da dogaro da rangwame daga Allah, bilhasali ma dai mun wajabta haka ne
wannan kuwa abu ne tabbatacce a wajiban addini da kuma a gurin hankali.
Idan kuwa biyayya gare shi bata wajaba ba a kan
haka to kuwa wannan ya saba wa annabci wanda babu makawa tana tare da wajabcin
da'a dimin da'iman. Idan kuwa ya zamanto duk abinda ya auku daga gare shi muna
jin cewa imma daidai ne imma kuskure to bai wajaba a yi masa da'a a kan kome
ba, sai fa'idar aiko Annabawa ta zamanto ta tafi haka nan kawai Annabin kuma
sai ya zama kamar sauran mutane, maganarsa ba ta da wata kimar da za a dogara a
kanta da'iman kamar yadda biyayya gare shi ba za ta zama tilas ba. Ba ma za a sami kwanciyar hankali ba baki
daya game da maganganunsa da ayyukansa.1
Wannan kuma dalili ne da ke tabbatar da
cewa Isma na tare da Imami domin kaddara cewa shi zababbe ne daga Allah Ta'ala
don shiryar da mutane a matsayin halifan Annabi. Za mu yi karin bayani a fasali
game da Imamah.
A duba sharhin al-Makasid Juzu'i na
5 shafi na 50, da kuma al-Ganiyyatu fi Usuluddin shafi na 161.
Sayyid Murtadha ya ambata a cikin littatin Tanzihil Anbiya da nassi kamar haka:
"Asahabul Hadis da Hashwaiyawa sun halatta wa Annabawa aikata manyan
zunubai kafin a ba su Annabci. Daga cikinsu ma har akwai wadanda suka halatta
wa Annabawa aikata sabo hatta bayan karbar Annabcin in banda karya a kan
al'amuran shari'a, akwai ma wadanda suka halatta karyar amma da sharadin a
boyewa ba bayyanawa ba, akwai ma wadanda suka halatta a kowane hali, su
Mu'utazilawa kuwa sun haramta cewa Annabawa na aikata sabo babba ko karami
kafin annabci da kuma bayan ba su annabcin amma sun halatta aukuwar abinda bai
kai karamin zunubi ba gare su kafin annabci da kuma bayan annabcin amma sun yi
sabani a kan Shugaban Manzanni Muhammadu (S.A.W.A.) wasu sabi daga cikinsu
akwai wadanda suka ce zai iya aikata kananan ayyukan sabo haka nan da gangan,
daga cikinsu kuma akwai wadanda suka ce ata tau sam annabawa ba sa taba aikata
wani abu da suka san cewa sabo ne sai dai kawai fuskar ba shi wata ma'ana ta
dabam. An hakaito daga Nizam da Ja'afar Bin Mubasshir da kuma wasu jama'a da
suka bi su a kan cewa aikata sabo daga gare su ba ya yiwuwa sai dai a kan
mantuwa da rafkanuwa kuma za a kama su da haka koda kuwa an yafewa al'ummunsu
saboda karfin saninsu da kuma martabarsu.Tanzihul Anbiya: Gabatarwa.
Ma'anar Isma a luga ita ce: Abu da
ke kange mutum daga wani abu wato kamar ya kange shi daga aukuwar wani abu da
ba ya so. Akan ce wane ya yi isma da dutse idan ya yi kariya da shi, da haka ne
ake kiranta Isma wato fakewa a dutse don kariya da shi, ya zo a Lisanil Arab
cewa: "Isma ita ce kariya, a kan ce na kare wani sai ya karu, na yi kariya
da Allah idan har ya tsaru daga sabo da tausasawarSa.
Isma daga Allah Ta'ala kuwa ita ce: Muwafaka da ke kubutar da mutum daga abinda
da ya so idan har ya zamanto ya aikata aikin biyayya, kamar yadda muke mika
igiya ga mutumin da kogi yake kokarin dulmuyarwa ya kama ya tsira da ita, Allah
Ta'ala ya bayyana wannan ma'ana a littafinSa da cewa: "Ku yi riko da
igiyar Allah baki daya" Surar Ali Imran: 103. A nan abin nufi da igiyar
Allah shi ne addininsa.
Ya zo daga Imam Zainul Abidin (A.S.) cewa yayin da aka tambaye shi ma'anar ya
ce: Shi ne mai riko da igiyar Allah, igiyar Allah kuma shi ne Alkur'ani da
Imam, ba sa taba rabuwa har zuwa ranar tashin kiyama, Imam yana shiryarwa ne
zuwa ga Alkur'ani shi ma Alkur'ani yana shiryarwa zuwa ga Imam. Wannan shi ne
fadin Allah Ta'ala: "Lalle ne shi wannan Alkur'ani yana shiryarwa zuwa ga
wadanda suke su ne mafiya daidai " Surar Isra'i: 9.
Biharul Anwar Juzu'i na 25 shafi na 194 da kuma farko al-Makalat na Shaikh Mufid
Juzu'i na 4 shafi na 34. Da kuma Lisanul Arab Juzu'i na 12 shafi na 403 bayani
game "Asama".
1- Domin a cikin yin haka akwai kore ayar Alkur'ani wadda take kwadaitarwa da a
yi biyayya ga Manzon Allah (S.A.W.A.) cewa: "Kuma wanda ya bi Allah da
ManzonSa zai shigar da shi gidajen Aljanna wadanda koramu ke gudana a
karkashinsu." Surar Nisa'i: 13. da kuma fadin Allah Ta'ala cewa:
"Kuma wanda ya bi Allah da Manzon to wadannan suna tare da wadanda Allah
ya yi ni'ima gare su," Nisa'i: 69 da kuma fadinsa cewa: "Kuma wanda
ya bi Manzon Allah to Lalle ya bi Allah ne" surar Nisa'i: 80 da kuma:
"Lalle hakika gare ku daga Manzon Allah akwai kyawawan abin koyi ga duk
wanda ke kaunar Allah da ranar Lahira kuma ya ambaci da yawa" Surar Ahzab:
22 da kuma fadin Allah Ta'ala: "Kuma wanda ya bi Allah da ManzonSa to
lalle ya rabbonta da rabo mai girma". Surar Abzab: 71.
- Domin a cikin yin haka akwai kore ayar Alkur'ani da ke kwadaitar da biyayya
ga Manzon Allah (S.A.W.A.) cewa: "Kuma wanda ya bi Allah da ManzonSa zai
shigar da shi gidajen Aljanna da koramu ke gudana a karkashinsu." Nisa'i:
13
"Kuma wadanda suka yi da'a ga Allah da ManzonSa to wadan suna tare da
wadanda Allah ya yi ni'ima gare su". Surar Nisa'i: 69.
Siffofin Annabi
Mun yi imani da cewa, Annabi kamar yadda
ya wajaba ya zamanto ma'asumi haka nan ya wajaba ya zamanto yana da mafi
kamalar siffofin dabi'u da hankali wadanda mafifita sune jarumtaka, da iya
tafida jama'a, da shugabanci da hakuri, da karfin kwakwalwa da hazikanci, har
ya zamanto babu wani daga cikin mutane da zai yi kusa da shi a kan haka, domin
ba don haka ba da babu yadda Annabcin ya zamanto al'amuran duniya baki daya ba.
shugabaci a kan dukan halittu kamar kuma yadda ba zai yiwu ya zamanto ya tafi
da
Kazalika wajibi ne ya zamanto mai tsarkin
haihuwa dan halas, amintacce, mai gaskiya wanda yake tsarkakakke daga dukkan
miyagun dabi'u hatta kafin aiko shi saboda zukata su amintu da shi rayuka kuma
su juya zuwa gare shi hatta ma don ya cancanci wannan matsayi mai girma daga
Ubangiji.
Annabawa da Littafansu
Mun yi imani a dunkule da cewa dukkan
Annabawa da Manzanni a kan gaskiya suke, kamar yadda muka yi imani da
kasancewarsu ma'asumai tsarkakakku. Musanta Annabcinsu kuwa, da zaginsu, da yin
izgili da su yana daga kafirci da zindikanci, domin yin haka yana nufin karyata
Annabinmu wanda Ya ba da labari game da su da kuma game da gaskiyarsu.
Wadanda
aka sani daga cikinsu kuwa kuma aka san shari'o'insu kamar Annabi Adam (A.S.)
da Annabi Nuhu (A.S.) da Annabi Ibrahim (A.S.) da Annabi Dawud (A.S.) da Annabi
Sulaiman (A.S.) da Annabi Musa (A.S.) da Annabi Isa (A.S.) da sauran Annabawan
da Alkur'ani ya ambace su a sarari ya wajaba a yi imani da su a ayyane duk kuwa
wanda ya karyata daya daga cikinsu to ya karyata su baki daya kuma ya karyata
Annabinmu a kebance.
Kazalika ya wajaba a yi Imani da
littafansu da abinda aka saukar musu.
Attaura
da Linjila ko kuma Bebul Tsoho da Sabon Alkawarin da ke hannun mutane a wannan
zamanin ya tabbata cewa gurbatattu ne daga ainihin wadanda aka saukar saboda
abinda ya auku gare su na daga canje-canje da musanyawa, na daga kari da ragi
bayan zamanin Annabi Musa da Annabi Isa (A.S.) saboda wasan da ma'abuta son rai
da kwadayi suka yi da su. Bilhasali
ma dai yawanci ko kuma ma dukkaninsu mabiya ne suka kaga su; bayan su Annabi
Musa (A.S.) da Annabi Isa (A.S.) ba sa nan.
____________
"Ku ce mun yi imani da Allah da
abinda aka saukar gare mu da abinda aka saukar zuwa ga Ibrahima da Isma'ila da
Ishaka da Yakuba da Jikoki da abinda aka ba wa Musa da Isa da abinda aka ba wa
Annabawa daga Ubangijinsu, ba ma rarrabewa a tsakanin kowa daga cikinsu kuma mu
masu sallamawa ne a gare shi." Surar Bakara: 136
"Amma tabbatattu a cikin ilimi daga cikinsu da muminai, suna imani da abin
da aka saukar zuwa gare ka da abinda aka saukar kafin kai kuma suna masu tsai
da salla suna ba da zakka suna masu imani da Allah da ranar lahira wadannan za
mu ba su lada mai girma" Surar Nisa'i: 162.
Ya zo a ruwayoyi da hadisai cewa
adadin Annabawa ya kai dubu dari da ashirin da hudu da dari uku da ashirin da
uku daga cikinsu ne, ko kuma dari uku da ashirin da biyar a bisa sabanin ruwaya,
su kuma wadannan Annabawan sunan mafi yawansu bai zo a Alkur'ani ba. Allah
Ta'ala na cewa: "Kuma lalle hakika mun aika wasu Manzannin kafin kai, daga
cikinsu akwai wadanda muka ba ka
labarinsu daga cikinsu akwai wadanda ba mu ba ka labarinsu ba" Surar
Ghafir: 78.
Adadin wadanda sunansu yazo a Alkur'ani kuwa ashirin da shida ne kamar haka:-
1- Annabi Adam (A.S.): sunansa ya zo sau 18 a Alkur'ani, game da shi Allah
Ta'ala yana cewa: "Lalle Allah ya zabi Adama da Nuhu da zuriyar Ibrahim da
zuriyar Imran a kan dukkan talikai." Surar Al- Imran 33, Kamar Kuma yadda
ya zo da Kiran Bani Adam sau Bakwai,
2- Annabi Nuhu (A.S.): sunansa ya zo a Alkur'ani sau 43, game da shi Allah
Ta'ala yana cewa: "Kuma lalle Mun aika Nuhu zuwa ga mutanensa ya zauna a
cikinsu har shekaru dubu babu hamsin" Surar Ankabutu: 14.
3- Annabi Idris (A.S.): sunansa ya zo sau biyu a Alkur'ani, Allah Ta'ala Yana
cewa: "Kuma ka ambata Idris a cikin littafi Lalle shi ya kasance mai yawan
gaskiya Annabi" Surar Maryam: 56.
4- Annabi Hudu (A.S.): Sunansa ya zo sau goma a cikin Alkur'ani, game da shi
Allah Ta'ala na cewa: "Kuma zuwa ga Adawa dan'uwansu Hudu, ya ce ya
mutanena ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bautawa baicin Shi." Surar
A'araf: 69 da Surar Hudu: 50.
5- Annabi Salihu(A.S.): Sunansa ya zo sau tara a Alkur'ani, game da shi Allah
Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle Mun aika wa Samudawa dan'uwansu Salihu ku
bauta wa Allah sai suka zamanto bangarori biyu suna husuma." Surar Namli:
45.
6- Annabi Ibrahim(A.S.): Ambaton sunansa ya zo sau 69 a Alkur'ani, game da shi
Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle Mun aika Ibrahima kuma Muka sanya
Annabci da littafi a zuriyarsu..." Surar Hadid: 26.
7- Annabi Ludu(A.S.): sunansa ya zo a gurare 26 a Alkur'ani, game da shi Allah
Ta'ala yana cewa: "Kuma lalle Ludu tabbas yana daga Manzanni". Surar
Saffat: 133.
8- Annabi Isma'il(A.S.): Ambaton sunansa ya zo a gurare goma sha daya a
Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma Muka yi wahayi zuwa
ga Ibrahima da Isma'ila da Ishaka da Yakuba..." Surar Nisa'i: 163.
9- Alyasa'u(A.S.): Ambaton sunansa ya zo sau biyu a Alkur'ani, game da shi
Allah Ta'ala Yana cewa: "Da Isma'ila da Alyasa'u da Yunusa da Ludu kuma
kowanne Mun fifita shi a kan talikai."
10- Zulkifli(A.S.): An
ambace shi sau biyu a Alkur'ani. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma ka ambaci
Isma'ila da Alyasa'u da Zulkifli kuma duka suna daga zababbu." Surar Sad:
48
11- Annabi Ilyasu (A.S.): An
ambace shi sau biyu a Alkur'ani, Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle
Ilyasu tabbas na daga cikin manzanni." Surar Saffat: 123.
12- Annabi Yunus (A.S.): Ambatonsa ya zo sau hudu a Alkur'ani. Allah Ta'ala
yana cewa: "Kuma lalle Yunusa Tabbas yana daga cikin Manzanni." Surar
Saffat: 139.
12- Ishak (A.S.): Ambaton sunansa ya zo sau goma sha bakwai a Alkur'ani. Allah
Ta'ala Yana cewa: "Kuma mun yi Masa albishir da Ishaka Annabi daga cikin
Salihai." Surar Saffat: 112.
14- Annabi Yakub (A.S.): An ambaci sunansa sau goma sha shida a Alkur'ani.
Allah Ta'ala Yana cewa: "...Kuma Muka yi wahayi ga Ibrahima da Isma'ila da
Ishaka da Yakuba da Asbata da Isa..." Surar Nisa'i: 163
15- Annabi Yusuf (A.S.): Ambatonsa ya zo sau ashirin da bakwai a Alkur'ani.
Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma daga cikin zuriyarsa akwai Dawuda da
Sulaimanu da Ayyuba da Yusufa da Musa da Haruna kuma haka nan Muke sakamtawa
masu kyautatawa." Surar An'am: 84.
16- Annabi Shu'aib (A.S.): Sunansa ya zo sau goma sha daya a Alkur'ani. Game da shi
Allah Ta'ala Yana cewa:"Kuma ga Madyana dan'uwansu Shuaibu." Surar
A'araf: 85, Hud: 84, Ankabut: 36.
17- Annabi Musa (A.S.): Ambatonsa ya zo sau dari da talatin da shida a
Alkur'ani. Game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle tabbatacce Mun
aiki Musa da ayoyinMu kan cewa ka fitar da al'ummarka daga duffai zuwa ga haske
kuma ka tunatar da su game da ranakun Allah lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga
dukkan mai hakuri mai yawan godiya." Surar Ibrahim: 5.
18- Annabi Haruna (A.S.): Ambaton sunansa ya zo sau ashirin a Alkur'ani. Allah
Ta'ala yana cewa: "Kuma Muka ba shi Dan'uwansa Haruna Annabi daga
rahamarMu." Surar Maryam: 53.
19- Annabi Dawud (A.S.) Ambatonsa ya zo sau goma sha shida a Alkur'ani. Allah
Ta'ala Yana cewa: "Da Ayyuba da Yunusa da Haruna da Sulaimana kuma Mun ba
wa Dawuda Zabura." Surar Nisai: 163.
20- Annabi Sulaiman(A.S.): Ambatonsa ya zo sau goma sha bakwai a Alkur'ani.
Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle hakika Mun ba wa Dawuda da Sulaimanu
ilimi" Surar Namli: 15.
21 - Annabi Ayyuba (A.S.):
An ambace shi sau hudu a Alkur'ani. Game da shi Allah Ta'ala Yana cewa:
"Ibrahima da Isam'ila da Ishaka da Ya'akuba da Asbata da Isa da
Ayyuba." Surar Nisa'i: 163.
22- Annabi Zakariyya (A.S.): Ambatonsa ya zo sau bakwai a Alkur'ani. Game
da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Da Zakariyya da Yahya da Isa da Ilyasu
kowane yana daga Salihai" Surar An'am: 85.
23- Annabi Yahya (A.S.): Sunansa ya zo sau biyar a Alkur'ani. Game da shi Allah
Ta'ala Yana cewa: "Ya Yahya ka riki littafi da karfi kuma Mun ba shi
hukunci yana yaro." Surar Maryam: 12.
24- Annabi Isma'ila Sadikul Wa'ad (A.S.): shi wani Isma'ilan ne dabam banda dan
Annabi Ibrahim (A.S.). Game da shi Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma ka ambaci
Isma'ila a cikin littafi lalle shi ya kasance mai gaskiyar alkawari kuma ya
kasance Manzo Annabi." Surar Maryam: 54.
25- Annabi Isa (A.S.): Sunansa ya zo sau ashirin da shida a Alkur'ani. Game da
shi ne Allah Ta'ala Yake cewa: "Lalle abin sani kawai shi ne cewa
Al-Masihu Isa dan Maryama Manzon Allah ne kuma KalmarSa. Ya jefa ta zuwa ga
Maryama..." Surar Nisa'i: 171.
26- Annabi Muhammadu (S.A.W.A.): Ambatonsa da sunan Muhammad ya zo sau hudu a
Alkur'ani, da Ahmad kuma ya zo sau daya. "Kuma Muhammadu bai kasance ba
face Manzo kuma Manzanni sun gabata kafin shi." Surar Al-Imran: I 44.
Daga cikin Annabawa akwai wadanda aka kawo siffofinsu ba sunayensu ba a
Alkur'ani. Allah Ta'ala na cewa: "Shin ba kaga wasu mashawarta ba daga
Bani Isra'ila bayan Musa, yayin da suka ce ga wani Annabinsu, nada mana wani
sarki mu yi yaki a tafarkin Allah". Surar Bakara: 246.
Su Manzannin an rarraba su ne an aika su zuwa ga al'ummu dabam daban a zamunna
dabam-daban. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle hakika Mun aika Manzo ga
kowace al'umma". Surar Nahl: 36.
Wasu Annabawa da Manzannin kuma an fifita su a kan wasu: Allah Ta'ala Yana
cewa: "Wadancan Manzannin Mun fifita wasunsu a kan wasu daga cikinsu akwai
wanda Allah Ya yi masa magana; kuma Ya daukaka sashensu a daraja." Surar
Bakara: 253
"Kuma lalle hakika Mun fitita wasun Annabawa a kan wasu kuma Mun ba wa
Dawuda Zabura." Surar Isra'i: 55.
Mafifita daga cikin Annabawa da Manzanni su ne Ulul Azami su biyar wadanda game
da su Allah Ta'ala ke cewa: "Kuma yayin da Muka karba daga Annabawa
alkawarinsu da kuma daga gare ka da kuma daga Nuhu da Ibrahima da Musa da Isa
Dan Maryama kuma Mun karba daga gare su alkawari mai tsanani." Surar
Ahzab: 7.
"Don haka ka yi hakuri kamar yadda ma'abuta karfin himma daga Manzanni
suka yi hakuri." Surar Ahkaf: 35.
Kuma sananne ne cewa himmar Annabawa ta sha bamban, ba daya take ba a gurin
dukkaninsu kamar yadda Allah Ta'ala ke bayyana haka da cewa: "Kuma lalle
hakika mun yi alkawari ga Adam kafin wannan sai ya manta kuma ba Mu sami karfin
himma gare shi ba." Surar D.H.: 115.
Mafificin Annabawa da Manzanni baki daya shi ne cikamakinsu, Annabi Amintacce
Muhammad Dan Abdullahi (Tsira da Amincin Allah su tabbata gare shi da zuriyarsa
tsarkakku). A duba Biharul Anwar Juzu'i na ll shafi na 77 da kuma Alkhisal. Al-
Amali Shaikh Mufid, da Kanzul Ummal, 32276, 32277, 32282, da sauransu, da
Tafsirin Al- Mizan Juzu'i na 2, da Mizanil Hikma Juzu'i na 7 da dai sauransu
Takaicen tarihin Manzo s.a.w.a
Sunansa da nasabarsa
:Muhammad dan Abdullahi dan Abdulmudallibi dan Hashimi dan Abdu manafi dan
kusayyi dan kilabi, nasabarsa madaukakiya tana tukewa zuwa ga annabi Ibrahim
(AS).
Mahaifiyarsa :ita ce Aminatu ‘yar wahabi dan Abdu Manafi dan Zuhrata dan kilabi.
Alkunyarsa :Abul kasim, Abu ibrahim.
Lakabinsa :Almusdafa , yana da sunaye da
suka zo a cikin alkur’ani mai girma kamar:khataman nabiyyin, Al’ummi ,
Almuzammil , Almudassir , Annazir , Almubin , Alkarim , Annur , Anni’ima ,
Arrahma , Al’bdu , Arrauf , Arrahim , Asshahid , Almubasshir ,Annazir , Add’ai
da sauransu.
Tarihin haihuwarsa:17 Rabiul auwal
shekarar giwa(571m)bisa mashhurin zance gun shi’a, an ce 12 ga watan da aka
ambata.
Wurin haihuwarsa:Makka.
Aikoshi :an aiko shi a Makka 27 rajab
yana dan shekara arbain.
Koyarwarsa :ya zo da daidaito tsakanin
dukkan hAlitta da ‘yanuwantaka da rangwame na gaba daya ga wanda ya shiga
musulunci, sannan ya kafa shari’a madaukakiya da dokoki na adalci da ya karbo
daga wajan Allah su kuma musulmi suka karba daga gare shi.
Mu’ujizozinsa :mu’ujizarsa madauwamiya
ita ce alkur’ani amma wadanda suka faru a farkon musulunci suna da yawa ba sa
kuma kirguwa.
Kiransa :ya kira mutane zuwa ga tauhidi
a makka a boye shekara uku ya kuma kira su a bayyane shekara goma.
Hijirarsa :ya yi hijira daga Makka zuwa
Madina a farkon watan rabiul auwal bayan shekara 13 daga aikensa, wannan ya
faru ne sakamakon cutarwa daga kafirai gare shi da kuma ga sahabbansa.
Yakokinsa :Allah ya yi wa manzo izinin
yakar mushirikai da kafirai da munafukai, sai ya yi dauki ba dadi da su a
wurare da yawa da mafi girmansu sune :Badar- Uhud- Al-khandak(ahzab)- Khaibar-
Hunaini.
Matansa:Khadija ‘yar khuwailid ita
ce matarsa ta farko, amma sauran sune :Saudatu ‘yar Zami’a da Aisha ‘yar Abubakar
da Gaziyya ‘yar Dudan (Ummu sharik) da Hafsa yarUmar da Ramla ‘yar Abu sufyan
(ummu habibia) da Ummu Salama ‘yar Abu Umayya da Zainab ‘yar Jahash da Zainab
‘yar Huzaima da Maimuna “yar Al-haris da Juwairiyya ‘yar Al-haris da Safiyya
‘yar Huyayyi dan Akhdabl.
‘ya’yansa :su ne 1- Abdullah 2-Al-kasim 3-Ibrahim
4-Fadima (AS) a wani kaulin da Zainab da Rukayya da Ummu Kulsum.
Ammominsa :su tara ne su ne ‘ya’yanAbdulmudallib :Al-haris da Zubair da Abu
Dalib da Hamza da Al-Gaidak da Dirar Al-mukawwam da Abulahab da Abbas.
Ammominsa mata :su shida ne daga iyaye mata daban daban su ne :Amima da
Ummu hakima da Barra da Atika da Safiyya da Arwa.
Wasiyyansa goma sha biyu ne su ne:Amirulmuminina Ali (AS) da
Al-hasan dan Ali da Al-husaini dan Ali da Aliyyu dan Husaini
da Muhammad dan Ali da Ja’afar dan Muhammad da Musa dan
Ja’afar da Ali dan musa da Muhammad dan Ali da Ali dan Muhammad da alhasan dan
Ali da Hujjat dan Al-hasan Al-mahadi (Allah ya gaggauta bayyanarsa).
Mai tsaron kofarsa :Anas dan Malik
Mawakansa:Hassan dansabita da Abdullahi dan Rawahata da ka’abu dan malik.
Mai kiran sallarsa:Bilal al-habashi da Dan ibn ummu maktum da sa’ad al-kirdi
Hatimin zobensa:(Muhammadur rasulullah).
Tsayin rayuwarsa :shekaru 63.
Tsayin lokacin annabtarsa :shekaru 23.
Tarihin wafatinsa:28 safar11 H.
Wajan da ya yi wafati:madina.
Inda aka binne shi:madina a masallaci madaukaki mai alfarma.