me ya sa muke bukatuwa zuwa ga addini?
Allah madaukaki yaa cewa a ckin Alkur'ani maigirma,"ka tsaida fukarka ga addini mikakke shine halittar da Allah ya halicci mutane akanta."Rom:'30
Abin da ake nufi da Addini shi ne wasu ilimomi da dokoki ne da Allah ya kafa ya aiko manzonsa da su domin shiryar da a'lumma. Wadannan dokoki kuwa sun kun shi abubuwa guda uku kamar haka:
1-Akida 2-kyawawan dabi'u 3 hukunce- hukunce.Abin da muke so mu yi magana akansa anan shi ne abin da ya shafi akida wato bangare na farko kenan. Amma kafin mu cigaba da bayani akan sa zamu fara da wasu abbuwa wato bukatuwa zuwa ga addini da kuma fa'idarsa.
Mutum a cikn wannan duniya ba'a halicce shi ba haka nan ba tare da wata manufa ba, domin kuwa Allah mai hikima ne ba ya yin wani abu wanda babu hikima a cikinsa. Domin idan ya kasance halittar mutum an yi ta ne ba tare da wani hadafi ba to lallai wannan zai zama kenan abu ne wanda ba bu hikima a cikinsa. Allah kuwa ba ya yin abu marar hikima don haka halittar mutum tana da manufa.
ya zo da yawa daga cikin ayoyin alkur'ani maigirma cewa Allah madaukaki ya halicci dan Adam ne domin ya samu kamala da cin nasara duniya da lahira.Saboda haka isa ga wannan hadafi kuwa yana bukatar tsari da dokoki wdanda zasu taimaka wa mutum zuwa ga wannan hadafi.Sannan kuma mutum, yana da bukatuwa zuwa ga dokoki wadan da zasu sa ya samu kwanciyar hankali da tsoro a cikin rayuwarsa ta duniya tare da 'yan'uwansa mutane.Tabbas kasancewar mutum mai takaitaccen ilimi da tunani ba zai iya tsara wa kansa wadannan dokoki ba. Don haka mutum yana da bukatuwa zuwa ga wanda ya san matsalolinsa da abin da yake bukata, don ya tsara masa hanyar da zai bi don ya cimma wannan hadafi nasa.Saboda haka tun da mun san cewa mutum ba wai kawai hadafin rayuwar duniya yake da shi ba, ya hada harda na gobe kiyama wato mutum yana so ne ya ci nasarar rayuwarsa duniya da lahira, babu kuwa wanda yasan abin da zai sa mutum ya cimma wannan sai wanda ya halitta shi kuma ya san abin yake bukata, wannan kuwa ba kowa ba ne face Allah mahaliccin kowa da komi.
Saboda haka kamar yadda muka fada a baya cewa addini ba komai ba ne face wadannan dokoki da tsari wadan da zasu taimaka wa mutum domin cimma wannan gurin nasa. Don haka kenan mutum yana bukatuwa zuwa ga addini.
Fa'idar addini ta kasu zuwa gida biyu:1-Fa'idarsa ga mutum a matsayinsa shi kadai ba tare da la'akari da waninsa ba.2-fa'idarsa ga mutum a matsayinsa wanda yake rayuwa a cikin mutane.
Faidar addini ga mutum a matsayinsa na shi kadai kusan a ce a bayyane yake, don haka muna iya takaitasu a cikin jumala guda uku.1-samar da natsuwa ga mutum.2-karfafa ruhin Dan-Adam.3-kare kutum daga sauran matsaloli.
Natsuwa: Amma dangane da natsuwa ga mutum, Allah madaukaki yana cewa a cikin kur'ani,"Wadan da suka yi imani zuciyarsu tana natsuwa da ambaton Allah, lallai ambaton Allah yana natsar da zuciya."ra'ad:28.
Lallai daya daga cikin fa'idar addini ga ko wane mutum ita ce, tana sanya mutum ya zama ya yi imani da Allah wanda yake shi ne, hakika wadda ba ta canzawa, sannan kuma shi ne mahaliccin kowa da komi wanda yake baiwa bayinsa ni'imomi marar karewa. Allah shi ne wanda dukkan alkhairai da rayuwa suke a hannunsa, yin Imani da haka ga mutum yakan sanya zuciyarsa ta samu natsuwa. Lallai duk wanda yake da Allah yana da komi, don haka wanda ya yi Imani da Allah ba ya tsoron komi sai shi kadai Allah madaukaki don shi kadai yake iya yin komi. Da haka ne sai mutum ya samu natsuwa ta musamman a cikin zuciyarsa.
Karfin zuciya: Addini yakan sanya mutum ya zama yana da karfin zuciya ta yadda zai samu dammar ya fi karfin son zuciyarsa, Allah madaukaki dangane da iyalan Imam ali a.s. yana cewa: "Suna cika alkawalin da suka yi, sannan suna tsoron ranar da sharrinta a warwatse yake. Sannan suna ciyar da abinci bisa suna son shi ga mabukata, marayu da bursunonin yaki. Lallai muna ciyar da ku saboda neman yardar Allah, kuma ba mu neman sakamako daga gareku ko godiya." Dahr:7-9.
Lallai irin wadannan siffofin suna samuwa ga zuciyar mutum sakamakon addini ta yadda ruhin mutum zai yi karfi sannan ya samu imani da kudrar Ubangiji wadda ba ta gushewa, sannan ruhi mai rauni ba zaya taba iya samu irin wadannan siffofi ba na kamala. Ruhin da yake damfare da Allah shi ne ruhi mai karfi wanda idan za'a dora rana a tafin hannunsa wata a bayan hannunsa ba zai bar abin da yake akai ba na madaukakin hadafi.
kariya ga mutum:daya daga fa'idojin addini shi ne, addini yakan kiyaye mutum daga shiga wani hali na kaka na kayi wanda zai iya nisantar da shi daga siffofi na gari.Addini yakan kiyayen mutum wanda ya yi Imani da ranar kiyama daga dukkan abubuwan da Allah zai yi fushi da shi wanda sakamakon hakan zai zama mutumin banza a cikin al'umma.Saboda haka mumini ba ya zaluntar kowa yana kiyaye hakkokin jama'a. Imam Ali a.s yana cewa:" Ina rantsuwa da Allah, in kasance ina kwana bisa kaya ko ina daure a cikin sarkoki ya fi mani soyuwa akan in wayi gari ranar kiyama in hadu da Allah da manzonsa ina matsayin na zalunci wani daga cikin bayin Allah ko na ci dukiyar wani ba tare da hakki ba. Imam ya cigaba da cewa da za'a bani sammai bakwai da abin ke cikinsu akan in kwaci fatar alkama dake bakin tururuwa ba zan amsa ba."
Don haka addini yakan sa mutum ya maida al'amarinsa zuwa ga Allah wanda sakamakon haka ne zai samu natsuwa, da haka ne kuma zai samu kariya daga ayyukan assha.
Lallai idan mutum ya kama addini gaskiya to lallai zai isa zuwa ga nasarar duniya da lahira wadda yake guri.Don haka addini yana da fa'idoji na duniya da lahira, wato mutum sakamakon addini zai samu nasarar rayuwarsa duniya da lahira.Addini yakan sa mutum ya zama yana dogara da kansa kuma ya samu karfin ruhi da natsuwa, sannan ya samu kariya daga munanan dabi'u. Sakamkon haka sai ya samu rayuwa mai kyau da kwanciyar hankali. Allah madaukaki yana cewa:"Duk wanda ya yi aikin kwarai namiji ne ko mace kuma alhalin yana mumini, to zamu rayar da shi rayuwa mai kyau, sannan kuma zamu saka masa da mafi kyau daga abin da suka kasance suna aikatawa."Nahl:98
Amafanin addini ga rayuwar zamantakewa: mutanen da suke rayuwa tare suna samun amfani ko cutarwa, kuma suna samun daukaka ko kaskancin duk tare.su ne ake cema al'umma.Al'umma ta gari kamar mutum daya na gari take, sannan tana da hukuncin mutum guda ne.saboda haka dole ne a samar da wasu ginshikai guda uku kafin a samu kyakkyawar al'umma wadda zata iya cin amfanin rayuwa kamar yadda ya kamata.Wadannan ginshikai kuwa su ne kamar haka:
1- Hadin kai da tausayawa juna.
2- Kaucewa cutar da juna.
3- Taimakon juna akan gaskiya.
Addini da imani da Allah da ranar kiyama su ne zasu iya samar da wadannan ginshikai guda uku kamar yadda muka fada a sama.
Amfanin addini na farko a zamantakewa ko rayuwar al'mma shi ne samar da hadin kai sakamkon akida guda, sannan shi ne abu mafi tasiri wajen samar da so da kauna a tsakanin mutane da kuma amince wa juna. Anan Allah T.A yana cewa:"ku riki igiyarAllah baki daya kada ku rarraba, sannan ku tuna ni'imomin da Allah ya yi a gareku yayin da kuka kasance makiyan juna ya hada zukatanku kuka wayi gari sakamakon ni'imarsa kuna "yan'uwan juna. Aali imran;103.
Daya daga cikin fai'dar addini shi ne addini yakan kawar da dukkan matsalolin dake damuwar al'umma wadan da sukan kai al'umma zuwa ga tabewa .
A kan haka ne Allah maigirma yake cewa: "Lallai Allah yana umurni da adalci da kyautatawa da kuma soyayya ga makusanta,sannan yana hani ga alfasha da abin ki da zalunci, yana yi muku wa'azi ne ko kun wa'aztu" Nahl:90
Fa'idar addini ta uku ga al'umma, addini yana kira ga al'umma da kyautatawa da taimakon juna da alkhairi sannan da hadin guiwa wajen aiwatar da ayyukan da zasu amfani dukkan jama'a. sannan yana hanin alumma daga aikata dukkan abin da zai jawo wa al'umma masifa da shiga halin kaka na ka yi.A kan wannan ne Allah T.A yake cewa a cikin littafinsa mai tsarki." Ku yi taimakon juna akan bin Allah kada ku yi taimakon jun akan sabon Allah da zalunci, Sannan ku ji tsoron Allah, lallai Allah mai tsananin azaba ne.
A tkaice addini yana kunshe da abubuwan da zasu kai ga al'umma baki daya zuwa ga cin nasara a rayuwarsu ta duniya da lahira.
Ya zuwa yanzu mun yi bayani kan bukatuwar mutane zuwa ga addini, don haka yanzu zamu koma zuwa ga asalin maganarmu wanda iata ce akidar shi'a a takaice. Amma kafin mu shiga cikin bayani kan akidojin dole a kula da wasu abubuwa kamar haka:
Dole ne mu samu yakini dangane da ginshikan addini:
Kamar yadda muka yi bayani a farkon littafan fiqh cewa dole ne kowane mutum ya samu yakini da tabbas a kan dukkan abin ya shafi akida ba kawai ya dogara ba da abin da wanin sa ya gaya masa ba. Wato dukkan abin da ya shafi akida dole ne mutum ya yi bincike daya bayan daya ta hankali da nassin kur'ani da hadisi har ya samu yakini. Ba kamar fiqhu ba wanda mutum yana iya dogara da maganar wani malami masanin fiqhun , ba dole ne ba sai ya je ya gano aya ko hadisi wanda yake magan akan wannan abin, fadar malamin da yake taklidi da shi kawai ta isar masa hujja a wajen Ubangiji.Amma dangane da akida ba haka ba ne, wajibi ne ga kowa ya tabbatar da gaskiyar ginshikan addini ta hanyar hankali ko nassi kamar yadda muka yi bayani a sama.
Me ya sa ba a taklidi a cikin akida?
Abin da yasa malaman addini musamman marja'ai suka ta fi akan cewa ba 'a yin taklidi a cikin akida, taklidi ya takaita ne kawai akan abin da ya shafi hukunce-hukunce
Saboda kamar yadda ayoyi da ruwayoyi suka zo akan cewa, lallai mutum wajibi ne ya samu yakini akan abin da ya shafi akida, ta hanyar taklidi kuwa ba za' a iya samun yakini ba, domin kuwa malami idan ya gaya maka cewa, misali dariya tana bata salla kuma ka yi aiki da shi anan ba wai yakini ka samu ba akan hakan duk da cewa idan ka yi aiki da hakan ya yi, amma ba ka samu tabbas ba, kawai ka dogara da shi ne domin ka san baya yin karya. Amma idan kana so ka samu yakini shi ne ka je ka yi bincike da kanka har ka gano inda Allah ya yi umurni da hakan, sannan ne ka samu yakini akan hakan.To a cikin abin da ya shafi hukunce-hukunce an yi mana rangwame cewa muna iya yin koyi da wasu masana akan hakan . Amma abin da ya shafi akida dole ne mu yi bincike da kammu har mu gano hakan. Urwatul wuthka: babin taklidi mas'ala ta 65.
Suratul Nahl:106--- Hujuraat:14 dukkansu suna dauke da bayanin hakan.
Ban da ma hakan samun yakini akan abin da ya shafi akida yana daya daga cikin siffofin kamala na ruhi mutum ta yadda zai san abin da shafi Allah da siffofinsa madaukaka. Sannan yakan fitar da ruhin mutum daga cikin duhun jahilci zuwa hasken ilimi wanda hankali yana umurtar mu da yin hakan kuma yakan lissafa shi cikin siffofi kyawawa.